December 2, 2021

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Nijeriya: Ana Ta Fuskar Iftila’i Da Annoba Kala-kala A Wannan Ƙasa – Sarkin Kano.

Page Visited: 382
0 0
Read Time:1 Minute, 17 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, yayi kira ga a kira ga al’umma su zama masu koyi da kyawawan ayyukan da magaba suka koyar domin samun sauki daga halin da Najeriya ke ciki.

Sarkin Kano yayi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron maukibin Qadiriyya karo na 71 da aka yi ranar Asabar a birnin Kano.

Inda sarkin ya ce, “babu shakka zamani yayi nisa abubuwa sun cancanza amma wannan ba zai hanamu koyi da abubuwa masu kyau na Alkairi da magabatanmu suka gabatar ba, don haka muna kira ga dukkan al’umma su zama masu koyi da su”.

Tin da farko da yake jawabi shugaban darikar Qadiriyya na Afrika Sheikh Abdulkadir Qariballahi Sheikh Nasiru Kabara ne yayi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari  da ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da kuma tsadar rayuwa da ake dama dasu Najeriya.

Game da hakan sarkin Kano ya ce, “Kamar yadda Khalifa ya fada ana ta  fuskar Iftila’i da annob kala-kala a wannan kasa don haka muna kira ga al’umma da malumanmu da a cigaba da addu’a Allah ya kawo mana ƙarshen abubuwa da suke damummu”.

Sarkin ya kuma yi kira ga al’umma “su canza halayen su abubuwa, da suka san suna yi wanda a addininmu da dabi’un al’adunmu basu aminta da su ba, yakamata lallai a rage kuma a daina yi domin mu samu aminci daga mahiliccin mu, a cewar Sakin Kano.

Taron da ya samu halartar manyan baki daga ƙasashen ketare da jihohin kudancin Najeriya da arewacin kasar.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *