Kwamitin gudanar da zaɓen Ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi wato NUBASS a matakin ƙasa ta gudanar da zaɓen ta wanda ta sabayi duk shekara.
Shugaban kwamitin zaɓen Kwamaret Abdullahi ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana la’akari da irin yadda ɗalibai suka bada haɗin kai har akayi zaɓen batare da tsaiko ba.
Abdullahi ya kuma gabatar da takardar shaidar nasara ga dukkanin ƴan takaran da suka lashe zaɓen a lokacin da suke karɓan rantsuwa.
Kwamaret Adamu Dauda Yashi wanda ya fito daga Jami’a mallakin jihar Bauchi dake Gaɗau BASUG shine yayi nasarar lashe kujerar shugabancin ƙungiyar.
A karon farko kenan da ɗalibi daga Jami’ar Jihar Bauchi ya zama shugaban ƙungiyar NUBASS a matakin ƙasa wanda kuma sauran ɗalibai suna kyautata zaton zai kawo sauyi mai ma’ana a ƙungiyar.
A jawabinsa na godiya Kwamaret Adamu Dauda Yashi ya bayyana godiyar sa wa Ubangiji da kuma ɗaukacin magoya bayan sa bisa irin ƙauna da ƙwarin gwiwa da suka nuna masa.
Yashi kuma bayyana cewa a shirye yake yayi aiki tare da kowa da kowa ba tare da nuna wani banbanci ba wadda acewarsa ta hakanne za a iya fafaɗo da martabar ƙungiyar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotu Ta Daure Wani Matashi Watanni 15 Kan Shiga Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi M.A.
-
Amaryar Ta Rasa Idonta Daya Ne Ana Tsaka Da Bikinta Sai Dai Duk Da Haka An Daura Mata Aure Da Angonta.
-
Zargin Taimakawa Ta’addanci: SSS Sun Mamaye Hedikwatar Babban Bankin Najeriya.
-
Gwamna Bala ya sha alwashin inganta tsaro, yaƙi da talauci, yayi yaƙin neman zaɓe a Itas
-
Ciyar Da Jihar Bauchi Gaba Ne Muradin Mu, Ku Sake Ba Mu Dama – Saƙon Gwamna Bala Ga Al’umar Udubo