SABUWAR JIHAR BAUCHI: Gwamna Bala a shekaru uku (I)

Page Visited: 252
0 0
Read Time:4 Minute, 12 Second

Daga Lawal Mu’azu Bauchi

 

Farawa da ayyukan raya ƙasa da samar da romon dimokraɗiyya na gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad na jam’iyyar PDP da ta cika shekaru uku masu ɗauke da ɗumbin nasarorin da suka cancanci yabo, kamar yadda hanci bai san daɗin gishiri ba, haka wasu sassan jihar mu ta Bauchi ba su ɗanɗana romon dimokraɗiyya ba sai zuwan Jagaban Katagum a matsayin gwamnan su.

” Duba mini hanya” magulmacin makaho ya faɗawa ɗan jagoran sa, duk da ƙarancin kuɗaɗe da tsadar rayuwa da kuma matsatsin tattalin arziki da duniya ke ciki a yau, rashin jini, rashin tsagawa. Gwamnatin Sanata Bala Muhammad ba tayi ƙasa a guiwa ba wajen gudanar da ayyukan tarihi a fannoni da kuma sassa daban-daban.

WUTAR LANTARKI:

Samar wa tare da gyara wuta a yankunan karkara na cikin muhimman ayyukan da gwamnatin jihar Bauchi ke ba su fifiko domin haɓaka tattalin arziki da samar da tsaro.

Wanda ba shi da doki, ba ya ƙyamar jaki. An shafe tsawon shekaru a wasu sassan jihar Bauchi ba tare da hasken wutar lantar ki ba, fitattu a ciki sun haɗa da Saɗe da yankunan ta a ƙaramar hukumar Darazo, wasu yankunan ƙananan hukumomin Ningi da Toro inda zuwa yanzu matsalar ta zama tarihi baya ga samar tare da raba manyan injinan raba wuta a yankuna daban-daban ciki har da unguwanni da yakunan fadar jiha.

TSARO:

Fanni mafi muhimmanci ga gwamnatin Sanata Bala Muhammad shine inganta tsaron rayuka da dukiyar al’umar jihar Bauchi da mazauna cikin ta.

Baya ga samar da kayan aikin inganta sashen da suka haɗa da samar da nagartattun motocin sintiri ga dukkanin jami’an tsaro, Gwamna Bala Muhammad ya samar da tsari na musamman da haɗin guiwar masu riƙe da sarautun gargajiya, malaman addinai da ƙungiyoyin fararen hula don magance ta-da-zaune-tsaye tare da tabbatar da hukunta waɗanda ke yi wa zaman lafiyar al’umar jiha zagon-ƙasa.

Aikin sanya fitillu akan hanyoyi na haifar da ɗa me ido wajen kula da shiga da fice da toshe maɓoyar ɓata-gari.

NOMA:

Sashen noma na duƙe tsohon ciniki na cigaba da bunƙasa cikin shekaru uku masu albarka na wannan gwamnati, baya ga ayyuka da dabaru na musamman don inganta harkar cikin yunƙurin magance yunwa, talauci da zaman kashe wando, gwamnatin jihar Bauchi ta ɗauki nauyin bada horo na musamman cikin dabarun zamani ga dubban matasa waɗanda yawancin su suka sami halartar kwasa-kwasai a wasu gonaki a jihar Nassarawa don dogaro da kai.

LAFIYA:

Cikin watanni biyu farko da zuwanta, gwamnatin jihar Bauchi ta jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Ƙauran Bauchi, Sanata Bala Muhammad ta ayyana dokar ta-ɓaci a sashen lafiya da nufin magance matsalolin da aka shafe shekaru ana fama da su da suka haɗa da wahalhalun rainon ciki da haihuwa, ƙarancin abinci me ɗauke da sinadaran ƙarfafa garkuwar jiki, mace-macen yara ƙanana da sauran su.

Ɗaruruwan ƙananan asibitoci gwamnatin ta gina, kwaskwarima da kuma samar da gadaje da kayan aikin jinya a ɗaukacin asibitocin jiha ba ya ga gina sabbin ɗakunan gwaji da kuma bincike.

ILIMI:

Jihar Bauchi a cewar alƙaluman ƙididdiga na shekarar 2018/19 ita ce jihar da tafi kowacce a Najeriya yawan yaran da ba su zuwa makaranta.

An ƙiyasta yara kimanin miliyan ɗaya da ɗoriya dake gararamba a tituna, lunguna da saƙo a jihar Bauchi a wancan lokaci.

Aikin mayar da yara ɗakunan karatu da ɗaukar nauyin su shine aikin da gwamna Bala ya fara da haɗin guiwar cibiyoyin agaji da tallafi na cikin gida da ƙasashen waje da suka da asusun kula da ilimin yara na majalisar ɗinkin duniya.

Ƙarkashin shirin, gwamnati ta gina dubban ɗakunan karatu a faɗin jiha tare da kwaskwarima wa tsoffi da ake da su da kuma ɗaukaka darajar wasu makaranti zuwa na musamman da nufin inganta rayuwar shugabannin gobe.

RUWA:

Kafin samar da dubban fanfunan burtsatse a faɗin jiha, Gwamna Bala Muhammad ya amince da biyan sama da Naira biliyan biyar na mashahurin aikin faɗaɗa samar da ruwa a fadar jiha da kewaye da haɗin guiwar Bankin Duniya.

Aikin wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya buɗe makwanni biyu da suka gabata yana tallafawa yaƙi da ƙarancin ruwa da aka ɗauki shekaru ana fama da ita.

TATTALIN ARZIKI:

Samar da walwalar shine ƙashin guiwar kowace gwamnatin dimokraɗiyya.

Bayan nazartar halin ƙunci da talauci da al’umar duniya ke fama da shi tun kafin ɓullar cutar murar mashaƙo da ta durƙusar da tattalin arziki, gwamnatin jihar Bauchi ta samar da shirin bada jari da tallafi don inganta rayuwar al’umar ta da kuma haɓaka tattalin arziki.

An yi wa shirin da ake kira Kaura Economy and Empowerment Program (KEEP) a turance, tsari na musamman da ƙarƙashin sa ake bada tallafin kuɗaɗe, babura, a daidaita sahu, injinan niƙa da na markaɗe, injinan bayin ruwa, awaki da kuma madarar kuɗaɗen jari.

Dubban mata da matasa a ƙananan hukumomi daban-daban sun ci moriyar shirin da ake sa ran zai yaƙi talauci da zaman kashe wando don bada al’umar damar dogaro da kai.

Muna tafe…

Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

2023: Ƴan Takarar Shugabancin Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya.

Ƴan Takaran zaben shugaban kasar Najeriya da za’ayi a shekara mai zuwa, yau sun rattaba hannu akan yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe da kuma tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Yayin wani biki da akayi a birnin Abuja da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranta, ‘yan takarar zaben da suka […]

Read More
Siyasa

Ƴan Sanda Sun Gargaɗi Masu Ɗauƙar Makamai Da Kayan Maye A Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar yan sandan jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya, ta ja hankalin yan siyasa bisa yaƙin neman zaɓe mai tsafta. Jan hankalin rundunar ya zo ne a dai dai lokacin da hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta buɗe damar yaƙin neman zaɓe a hukumance. Kwamishinan ƴan sandan […]

Read More
Siyasa

Kishin Ƙasa Shi Ne Tubalin Jagorancin Al’umma, Raunin Jagoranci Shi Ke Haifar Da Rashin Adalci,-Obasanjo.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce kasar na bukatar gwamnatin da ta san yadda ake gudanar da mulki. Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito tsohon shugaban na wannan maganar a wurin taron bikin cikar makarantar Kings college ta Legas – daya daga cikin tsoffin makarantu a kasar – shekara 113 da kafuwa. Mista […]

Read More