Daga Muhammad Sadik Umar
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce samarwa matasa aikin yi zai iya taimaka wajen rage matsalar rashin tsaro a jihar Kano dama Najeriya baki daya.
Sarkin Kano, ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakƙuncin shugabanin cibiyar Koyan Zayyanar Sadarwa IGC, ƙarkashin jagorancin Dakta Ibrahim Garba Danjuma a wata ziyara ta musamman da suka kai masa fadar sa.
“samarwa matasa sana’o”in abune daya dace a wannan lokaci da matasa suke ƙoƙarin shiga harkar bangar siyasa,” in ji Sarkin.
Ya kuma yabawa wanda ya samar da cibiyar domin taimakawa al’ummar jihar nan.
Da ya ke jawabin wanda ya jagoranci ziyarar Dakta Ibrahim Garba Danjuma, ya ce ya samar da makarantar ne domin nuna kishinsa da irin dawainiyar da gwamnati jihar kano take yi na kyautata rayuwar matasa inda shima yaga ya dace ya samar da cibiyar koyon sana’o’in a jihar Kano.
Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro da sakataren yaɗa labaran masautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya aikewa manema labarai.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotu Ta Daure Wani Matashi Watanni 15 Kan Shiga Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi M.A.
-
Amaryar Ta Rasa Idonta Daya Ne Ana Tsaka Da Bikinta Sai Dai Duk Da Haka An Daura Mata Aure Da Angonta.
-
Zargin Taimakawa Ta’addanci: SSS Sun Mamaye Hedikwatar Babban Bankin Najeriya.
-
Gwamna Bala ya sha alwashin inganta tsaro, yaƙi da talauci, yayi yaƙin neman zaɓe a Itas
-
Ciyar Da Jihar Bauchi Gaba Ne Muradin Mu, Ku Sake Ba Mu Dama – Saƙon Gwamna Bala Ga Al’umar Udubo