Saudiya Ta Fara Gasar Cin Kofin Duniya Da Kafar Dama Bayan Doke Argentina 2 Da 1.

Page Visited: 165
0 0
Read Time:1 Minute, 4 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.

 

Ƙasar Saudiyya ta zama ta ɗaya a teburin C bayan yin nasara a kan Argentina da ci biyu da ɗaya a wasan farko cikin rukunin C.

Argentina ce ta fara cin kwallo ta farko a bayan mintuna 20 da fara wasan ta hanyar fanareti da samu wanda ɗan wasan gabanta Messi ya buga.

An tafi hutun rabin lokaci Saudiyya na nema inda bayan dawowa daga hutun ta farke kwallo ta farko a minti na 48 ɗan wasan Saudiyya S.Alshehri ne ya ci kwallon.

Saudiyya ta sake cin kwallo ta biyu ne a minti 53 ta hannun S.Al-dawsari, an tashi wasan 2-1.

Wannan rashin nasara da Argentina ta yi ya sa ta zama ta ƙarshe a tebur cikin rukunin C.

Baki ɗaya an buga wasa na shiga kenan cikin gasar cin kofin duniya na 2022.

Ranar 26 ga watan Nuwamba Saudiyya za ta ƙara buga wasanta na biyu da ƙasar Poland, inda ita kuma Argentina za ɓarje gumi da Mexico.

An jima da ƙarfe biyu na rana agogon Najeriy, Danmark za ta kece raini da ƙasar Tunisiya cikin rukunin D, yayin Mexico za ta buga kara da Poland a rukunin C.

Da ƙarfe taran dare agogon Najeriya Faransa za ta yi gumurzu da ƙasar Australia.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Wasanni

Faransa Mai Ɗauke Da Kofin Duniya Za Ta Fara Kare Kofinta A Yau Talata

Daga Suleman Ibrahim Modibbo   Ƙasar Faransa mai dauke da kofin duniya za ta yi gumurzun kare kofinta da ƙarfe 8 ɗin daren yau a ƙasar Qatar a gasar cin kofin duniyar da ke gudana yanzu haka. Faransa ta ɗauki kafin ne a shekarar 2018 a ƙasar Rasha, bayan ta yi nasara a wasan ƙarshe. […]

Read More
Wasanni

A Halin Yanzu Tunisiya Ce Ta Ɗaya A Rukunin D Bayan Ta Yi Canjaras Da Denmark A Cigaba Da Gasar Cin Kofin Duniya.

  An kai ruwa rana tsakanin ƙasar Tunisiya da Denmark wanda hakan ya kai su ga tashi babu kwallo ko ɗaya a ragar ko wace ƙasa,, abinda ke nuni da cewa ƙasashen biyu suna tsaka mai wuya cikin rukunin D. Tunisiya za ta buga wasanta na gaba ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, inda […]

Read More
Wasanni

Amurka Da Wales Sun Raba Maki Ɗai-Ɗai Bayan Sun Yi Kunnen Doki.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Ƙasar Amurka da Wales sun tashi 1 da 1  a wasan farko da suka buga cikin rukunin B na gasar cin kofin duniya na 2022. Wannan dai shine wasa na biyar da aka buga a wasan a baki ɗaya cikin gasar da aka fara ranar Lahadin da ta gabata kuma wasa […]

Read More