Sharuɗɗan Sulhu Guda 10 Da Gwamnatin Zamfara Da Ƴan Bindiga su Ka Gindaya Wa Juna.

Page Visited: 433
0 0
Read Time:2 Minute, 58 Second

Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa sulhun da ta ƙulla da ‘yan bindiga a faɗin jihar ya na tasiri sosai, domin a cikin watanni 9 an saki fiye da mutum 3,000 da aka yi garkuwa da su, ba tare da an biya diyyar ko sisi ba.

Daga nan sai Gwamnatin Zamfara ta yi kira ga sojoji cewa a lalubo hanyar kawo ƙarshen rikicin ba tare da an yi amfani da ƙarfin makamai ba.

Yarjejeniyar Gwamnatin Zamfara Da ‘Yan Bindiga:

1. ‘Yan bindiga sun ce ba za su ajiye makamai ba sai gwamnati ta rushe ‘yan sakai.

2. Gwamnatin Zamfara ta yarda za ta samar da ababen inganta rayuwa a cikin Fulani kamar yadda aka samar a cikin garuruwa.

3. ‘Yan bindiga da iyayen su sun nemi a saki duk wani Bafulanin da ke hannun ‘yan sakai.

4. ‘Yan bindiga sun amince su saki dukkan waɗanda su ka yi garkuwa da su ba tare da sai an biya ko ƙwandala ba.

5. ‘Yan bindiga sun amince su miƙa makaman su cikin ƙanƙanin lokaci.

6. Cikin watanni 9 sun saki fiye da mutum 3,000 ba tare da an biya diyyar komai ba.

7. ‘Yan bindiga sun daina kai hare-hare a ƙauyuka da kasuwanni da gonaki.

8. ‘Yan bindiga sun miƙa bindiga samfurin AK47 sama da 1,000 da sauran ƙananan bindigogi da wasu makamai daban-daban.

9. Gwamnatin Zamfara ta haramta ƙungiyar ‘yan sakai.

10. Gwamnatin Zamfara ta fara gina wa Fulani makiyaya RUGA a Ƙaramar Hukumar Maradun.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga cewa daga 2011 Zuwa 2019 ‘yan bindiga sun garkuwa da mutum 3,672, an biya fansar naira biliyan 3, sun saka mata 4,983 zaman takaba, sun maida ƙananan yara 25,050 marayu -Rahoton Gwamnati.

Rahoton da Gwamnatin Jihar Zamfara ta fitar ya nuna cewa tsakanin watan Yuni 2011 zuwa Mayu 2019, ‘yan bindigar Jihar Zamfara sun karɓi sama da naira bilyan 3 kuɗin fansar mutanen da su ka riƙa yin garkuwa da su.

Haka kuma rahoton ya tabbatar cewa fiye da mutum 190,340 ne su ka rasa muhallin su sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga.

Rahoton wanda Kwamitin Bincike wanda Gwamna Bello Matawalle ya kafa cikin 2019 ya kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar, ya nuna cewa waɗannan shekaru takwas cikin mulkin tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari, mata 4,983 sun zama ‘yan takaba, bayan kisan mazajen su da ‘yan bindiga su ka yi.

Sannan kuma ‘yan bindiga sun maida ƙananan yara har 25,050 sun zama marayu bayan kisan iyayen su da aka yi.

Rahoton kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Matawalle, Sulaiman Zailani ya fitar, ya ce a shekarun takwas an sace shanun makiyaya Fulani guda 2,015, awaki da tumaki 141, jakai da raƙuma.

Wannan rahoto ya ƙara da cewa an lalata motoci da babura 147,800, waɗanda ko dai aka lalata ko kuma aka ƙone ƙurmus.

Yanzu Kashe-kashen Ya Ragu -Gwamnatin Zamfara:

Yayin da ake ci gaba da kashe mutane ana garkuwa da su tare da ƙaƙaba masu haraji a wasu yankunan jihar, har da hana manoma zuwa gona da cin kasuwanni, Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce kashe-kashe ya ragu a jihar da kuma garkuwa da mutane.

Sannan kuma ba a san yawan mutanen da aka kashe ko aka yi garkuwa da su ba a zamanin wannan gwamnatin ta Bello Matawalle.

Wannan rahoto dai bai bayyana adadin mutanen da aka kashe a waɗannan shekaru takwas ba. Kuma ba ya ɗauke da adadin ɓarnar da aka tafka daga Yuni 2019 zuwa Agusta 2022 zamanin mulkin Gwamna Bello Matawalle.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Tsaro

Mayakan ISWAP sun hallaka jami’an tsaro da farar-hula a Borno.

Mayakan jihadi sun kai hari sansanin soji da wani yankin Borno tare da kashe sojoji 9, da ‘yan sanda biyu da kuma farar-hula, kamar yada majiyoyin tsaro da mazauna yanki suka tabbatar. Mayakan IS sun farwa garin Malam Fatori, a ranakun daren Juma’a da kuma safiyar Asabar, a cewar majiyoyin. A cewar bayanan da aka […]

Read More
Tsaro

Kano: Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jawo Rasa Ran Mutum Guda Da Jikkata Wasu Biyar – Ƴan Sanda.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya inda kuma biyar suka jikkata sakamakon rikicin Manoma Da Makiyaya da ya afku a garin Kuka Bakwai, da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar. Rundunar yan sandan ta ce an samu ɓarkewar  rikicin ne […]

Read More
Tsaro

Masu Garkuwa Sun Bukaci A Basu Kudin Fansa Har Naira Miliyan 250 A Katsina Bayan Sun Sace Mutum 43.

Daga Suleman Ibrahim Maddibo wasu bayanai daga jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya na cewa, al’ummar kauyen Bakiyawa da ke yankin Batagarawa na cikin firgici bayan da ‘yan ta’addan da suka sace mazauna kauyen 43 suka bukaci da a biya su naira miliyan 250 a matsayin kudin fansa, kafin sako mutanen da suke […]

Read More