June 27, 2022

Shin Da Gaske Ne Buhari Ya Yi Kyautar Mota Ga Wani Bawan Allah?

Page Visited: 2006
0 0
Read Time:1 Minute, 7 Second

?Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Wasu rahotanni da jaridun Internet a Najeriya suka raiwato a ranar Asabar sun ce shugaban Najeriya Muhammd Buhari, ya yi kyautar mota kirar golf da kudin mai naira dubu ɗari bakwai, wanda suka ce wai  shugaban ne ya bayar ga wani  bawan Allah mai suna Malam Umar Small fire.

Rahotannin sun ce Small Fire, shine wanda ya ɗauki shugaba Muhammadu Buhari a motar sa ya kaishi gida yayin da Boko haram suka kai masa hari a unguwar Kawo da ke jihar Kaduna Arewa maso yammacin Najeriya, a shekarar 2014.

Cikin hutunan da ake yaɗawa a ƙasan labarin sun nuna wasu mutum biyu suna miƙawa mutumin ƙudi da takardu inda shi kuma mutumin yake karɓa.

Hotuna: Buhari ya kaddamarda fasahar 5G Network.

Sakon Buhari Ga Iyayen Marigayiya Hanifa.

Buhari Ya Bawa Dattawan Arewa Kunya -Hakeem Baba.

To Shin Da Gaske Buhari Ne Ya Yi Kyautar Motar?

Har zuwa wannan lokaci dai fadar gwamnatin Najeriya, ba ta ce komai game da labarin ba, kuma shi kansa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, bai ce komai ba,  hasalima har yanzu babu wani makusancin Buhari da ta tabbatar da gaskiyar labarin ko dai ƙaryatawa.

Tun da farko dai jaridun Internet ɗin sun dunga nuna bidiyon mutumin yana ya bayyana yadda ya tseratar da rayuwar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, tun kafin ya zama shugaban ƙasar Najeriya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *