January 19, 2022

SHIRIN AIKI DA ILIMI FITOWA NA UKU ( 3 )

Page Visited: 931
2 0
Read Time:1 Minute, 51 Second

Gabatarwa Malam Muhammad Sakibu Adam

Mai karatu assalamu alaikum, barkank da wannan lokaci, wanda da Martaba FM Radio online ke gabatar da shirin Aiki da Ilimi, shirin da hukumar gidan Radio martaba ya dauki dawainiyar kawo muku a duk ranakun Talata.

Fassarar littafin Ashmawi kashi na (3)

A yau in sha Allahu zamu dora akan bayanin ladaban biyan bukata.

Akwai ladabai da akeso ga duk wanda yaje biyan bukatarsa (gayadi ko bawali) da ya kula dasu domin ya samu yayi ingantaccen tsarki dan idan tsarki ya kyautata to ibada zata kyautata idan kuwa ba tsarki to ba ibada domin duk ibadar da mutum zaiyi in ba tsarki sunanta asara.

Daga cikin ladabin anaso ga mai biyan bukatarsa ya tabbatar da yayi addu’a kafin ya shiga makewayi yace: أللهم إني أعوذ بك من الخبث والخبائث da bayan ya fito yace: الحمد لله الذى أذهب عني الأذى وعافاني sannan kuma ya kula sosai wajan karkade duk abin da yafito daga mafita biyu (gaba ko baya).

Sannan idan yai bawali da gayadi a tare to ya tabbatar da cewa ya fara tsarkin bawali kafin yayi na gayadi kuma shima sai ya fara jiqa hannunsa da ruwa sannan yayi tsarkin bawali bayan ya gama sai kuma yayi na gayadi amma ya tabbatar ya dan sassauta duburarsa kadan yai numfashi saboda in ma da ragowa zai fito, kuma ya fara katseshi da yanki kafin ya zuba ruwa a duburarsa wajan tsarkin.

Sannan anaso ya buya daga idanuwan mutane, sannan ba’asan magana alokacin biyan buqata sai in da uzuri kwakkwara.

Kuma ya kula sosai wajan biyan bukatarsa kada ya biya bukatarsa a inda yake tsandauri (inda bawalin zai dinga fallatsar masa).

Sannan ana so ya raba cinyoyinsa wajan biyan bukatarsa kada ya hadesu.

Ana so mai biyan bukata ya nisanci rami kada ya biya bukatarsa acikin rami, ko idaniyar ruwa, ko kan hanya, ko inuwar mutane.

Hakana anaso ga mai biyan bukata ya fara gabatar da qafarsa ta hagu wajan shiga makewayi sannan ya gabatar da qafar dama wajan fitowa.

Ga mai son daukar nauyin wani shiri ko daba talla zaku iya samun mu a whatsapp 07030886603 ko ku kiramu kai tsaye.

Dan duba karatun baya shiga nan SHIRIN AIKI DA ILIMI FITOWA NA BIYU ( 2 )

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *