June 27, 2022

Shirye shirye sunyi nisa na kula da lafiyar ma’aikatan jihar Jigawa.

Page Visited: 363
0 0
Read Time:39 Second

Daga: Ashiru Gambo, Jigawa.

Asusun kula da lafiya na jihar Jigawa zai yi rigistar shiga shirin kiwon lafiya wa ma’aikatan jihar.

Sakataren asusun Dr Nura Ibrahim ne ya sanar da hakan ga manema labaru a birnin Dutse, fadar jihar Jigawa.

Yace za a fara rijistar ne a ranar 27 ga wata ga maaikatan da ke karkashin gwamnatin jihar sannan daga bisani a fadada shi ga maaikatan kananan hukumomi kana a kammala da ma’aikatan sashen ilmi da ke fadin jihar.

Dr Nura Ibrahim ya kara da cewar za a aike da takardar da ke kunshe da jadawalin tsarin rajistar zuwa ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar.

Yace a lokacin rajistar, ana bukatar kowane ma’aikaci da ya kawo bayanai da kuma karamin hoton matarsa da yayansa guda hudu wadanda ke kasa da shekaru 18.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *