December 2, 2021

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Shugaban Ɗariƙal Ƙadiriyya Yayi Umarni Ga Al’ummar Musulmi Su Gaggauta  Yankar Katin Zaɓe.

Page Visited: 2680
0 0
Read Time:1 Minute, 11 Second

Yayin da hukumar Zabe  ta kasa mai zaman kanta INEC ke cigaba da bayar da katin zabe na shekarar 2023 ga yan ƙasa.

Shugaban darikar Qadiriyya na Afrika Sheikh Abdulkadir Qariballahi Sheikh Nasiru Kabara, ya yi kira ga al’ummar Musulmi a Najeriya su hanzarta yankar katin zabe domin tarin amfanin sa.

Cikin wata zantawar da Martaba FM a jihar Kano Sheikh Abdulkadir Qariballahi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, ya  muna bukatar da ke akwai ga yan kasa wajen yin ayukka a aikace tare da yin aikin tukuru gami da addu’a ga kasa wanda a cewar sa ta haka ne kawai Najeriya zata samu cigaba mai dorewa, ‘ayi aiki a aikace kuma a hada da addu’a”.

Game da yankar katin zabe da tuni hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tayi nisa wajen yiwa yan kasa rajista Sheikh Qariballahi Kabara ya ce, mutane su yi maza su je su yi rajistar domin akwai Alkairi da addini ya tanadar game da yankar katin zaben kuma addini yayi umarni da yin hakan.

Daga karshe Malam Kabara ya yi kira ga al’ummar musulmi da suje su yanki katin zabe tare da jan hankalin mutane kan su yi amfani da katin zaben ta hanyar data da ce ” Ina kira aje a yanki katin zabe a kuma zaɓi shugabanni na kwarai”.

A ranar Talata  23 ga watan Nuwamba na shekarar 2021 ya rage saura kwanaki 451 a yi babban zaɓen Najeriya na shekarar 2023.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *