Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
TA'ADDANCI: 'Yan majalisun Nijar sun koka akan yadda 'Yan ta'adda ke kashe jama'a. - Martaba FM
October 20, 2021

TA’ADDANCI: ‘Yan majalisun Nijar sun koka akan yadda ‘Yan ta’adda ke kashe jama’a.

Page Visited: 115
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 48 Second

Wasu ‘Yan majalisun Jamhuriyar Nijar sun ce ‘Yan ta’addan dake kai hare hare suna kashe mutane a Yankin Tillaberi na cin karen su babu babbaka, duk da dokar ta bacin da gwamnatin kasar ta kafa a yankin.

 

Yan majalisun da suka fito daga Yankin sun yi kira ga gwamnatin Nijar da ta sake dabaru wajen daukar matakai masu karfi domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin dake iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso, kasashe biyu da suma suke fama da hare haren ‘Yan ta’addan.

 

Domin dakile yawan hare haren da ake samu a yankin, gwamnatin Nijar ta kafa dokar ta baci wadda ta hana amfani da babura da takaita sayar da man fetur da kuma rufe kasuwannin da ake zargin suna samarwa Yan ta’addar makamai.

 

Sai dai duk da daukar irin wadannan matakai, ‘Yan majalisun sun ce ana ci gaba da samun hare haren bindigogi da bama bamai daga ‘Yan ta’addar, wadanda ke barazana ga daukacin kauyukan yankin, ganin yadda suke yawo da makamai dare da rana ba tare da wani ya hana su ba.

 

Yan majalisun awani sanarwa da suka rabawa manema labarai sunce wadannan hare haren da ‘Yan ta’addan ke kaiwa akan babura yayi sanadiyar hallaka daruruwan fararen hula da sojoji, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

 

‘Yan majalisun sun ce a cikin wata guda kawai, fararen hula 98 aka kashe tare da jandarmeri 19 a yankuna 3 dake Jihar Tillaberi.

 

Wannan kisa na baya bayan nan da akayi a ranar litinin a kauyen Darey-Daye shine wanda ya ritsa da fararen hula 37 dake aiki a wata gona, kuma cikin su harda mata 4 da yara 13.

 

‘Yan majalisun sun bukaci gwamnati da ta kara yawan sojojin dake yankin da kuma kai agajin gaggawa a duk lokacin da aka fuskanci hari musamman wajen amfani da jiragen saman soji.

 

Sanarwar tace a halin yanzu ‘Yan ta’addan na kai hari har akan rakuma da kekuna, kana daga bisani su bata saboda hadin bakin da suke da shi da wasu mutanen dake cikin al’umma wadanda ke basu labarin  inda sojoji suke.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us