Wata kotun shari’ar Muslunci da ke Kano ta sake mayar da Murja Kunya gidan yari, to amma a wannan karon kotun ta haɗa da wasu matasa uku da suka haɗa da da Real Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da Sadiq Mai Waƙar A daidai ta nan zuwa gidan yari.
Freedom Radio ta rawaito cewa kotun ta sake aike wa da fitacciyar mai amfani da dandalin TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya da ƙarin wasu mutum uku zuwa gidan yari.
Mutanen sun haɗa da Babban abokin Murjan wato Ashir Idris da aka fi sani da Mai Wushirya sai kuma Aminu BBC da Sadiq Shehu Shariff wanda ya yi waƙar nan mai taken “A daidai ta nan”.
Zauren Malaman Kano ne ya yi ƙarar matasan bisa zargin wallafa bidiyoyin baɗala a dandalin TikTok.
Ana tuhumar Murja da Real Ashir Idris da yin bidiyon batsa a TikTok, inda ya amsa laifinsa yayin da ita kuma ta musanta.
An kuma tuhumi Aminu BBC da yin bidiyon batsa a dandalin TikTok wanda ya musanta.
Sai kuma Sadiq Shehu Shariff mai waƙar “A daidai ta nan” wanda aka zarga da yin waƙar batsa zargin da ya musanta.
A nan ne lauyoyinsu suka nemi a basu belinsu, sai dai lauyan Gwamnati ya yi suka, inda ya nemi a basu mako guda domin su yi martani.
Kotun ta tura su zuwa gidan yari har zuwa 23 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Dangane da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba, inda Kotun ta ce za ta yi nazari a zama na gaba.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Tinubu ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatinsa Akume
-
Kungiyar Ƴan Jarida ta ƙasa NUJ za ta bi sa sahun Kungiyar Kwadago NLC don Tsunduma yajin aiki kan cire tallafin Mai
-
Tsohuwar Ministar mata Pauline Tallen ta shiga hannun EFCC kan zargin Almundahana
-
Kotu Ta Bawa Ƴan Sanda Umarnin Kama Sheikh Idris Dutsen Tanshi Bisa Rainata.
-
Bayan Shan Rantsuwa Tinibu Ya Ce Daga Yanzu Gwamnatinsa Za Ta Soke Tallafin Man Fetur.