Daga Yusuf Ali
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya kafa tarihi wajen taka muhimmiyar rawar bai wa rundunar sojojin Nijeriya cikakken goyon baya domin tunkarar barazanar Boko Haram da wanzar da zaman lafiya a fadin jihar Yobe.
A hannu guda kuma, Gwamna Buni ya kafa rundunar ‘Rapid Response Squad’ Operation ‘Haba Maza’ tare da bayar da sabbin motocin Toyota Hilux guda 30 ga rundunonin tsaro da ke ayyukan samar da tsaro a jihar Yobe.
Baya ga wannan, Gwamna Buni ya bayar da gudumawar wani katafaren gini mai hawa daya cike da kayayyakin bukata a matsayin shalkwatar Rundunar Haba Maza a Damaturu.
Har wala yau, Gwamnatin Buni ba ta tsaya nan ba, inda ta ci gaba wajen tallafawa jami’an tsaron; Sojoji, Civil Defence, DSS da sauran bangarorin jami’an tsaro da ke aikin samar da tsaro a fadin jihar. Tare da sauran kungiyoyin tsaro na sa-kai kamar yan-banga da yan-sintiri da makamantan su, wadanda gwamnatin jihar ke tallafa musu da motoci, kudaden alawus da bukatun yau da kullum don tabbatar da ingantattun ayyukan tsaro.
Bugu da kari kuma, Gwamnatin Buni ta samar da wani tsarin ingantacciyar hanyar sadarwa tare da hada kan al’umma don inganta harkokin tsaro. Yayin da aka samar da wani dandali wanda al’umma da malaman addini ke zama domin tattaunawa da tsara manufofin da suka shafi tsaro da aiwatar da su.
A wani mataki na daban kuma, gwamnatin Gwamna Buni ta na gudanar da taron tattauna al’amurran tsaro lokaci zuwa lokaci tare da masu ruwa da tsaki a kowane bangaren al’ummar jihar Yobe, domin ba da shawara kan matakan da suka dace a dauka don magance matsalolin tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Yusuf Ali,
Babban Mataimaki na Musamman (SSA) a kan kafofin yada labaru na zamani & Dabarun Sadarwa ga Gwamna Mai Mala Buni CON.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotu Ta Daure Wani Matashi Watanni 15 Kan Shiga Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi M.A.
-
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Gargadi Mazauna Jihar Kan Atisayen Harbin Bindiga A Kalebawa.
-
Ba Zamu Lamunci Daba Da Shaye-Shaye A Unguwarmu Ba- Al`Ummar Dala.
-
Ayyukan Laifin Da Aka Aikata A Kano Cikin Shekarar 2022 Sun Ragu Fiye Da 2021- Ƴan Sanda.
-
Amaryar Ta Rasa Idonta Daya Ne Ana Tsaka Da Bikinta Sai Dai Duk Da Haka An Daura Mata Aure Da Angonta.