December 2, 2021

Tuba Abduljabbar Yayi Ko Kuma Salo Ya Sauya?

Page Visited: 231
0 0
Read Time:2 Minute, 36 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo.

Bayan yin mukabala wadda shi Abduljabbar din ya nemi gwamnatin jihar Kano ta shirya masa shi da malamai domin ayi masa adalci gwamnatin ta shirya masa mukabalar a ranar Asabar 10 ga watan Yuli na shekarar 2021.

Alkalin da ya jagoranci mukabalar ya bayyana cewa Abduljabbar bai amsa ko tambaya guda daga cikin tambayoyin da malamai hudu suka yi masa ba ya ragewa gwamnati tayi hukunci a kai.

Bayan kwana guda da yin mukabalar kwatsam sai aka ji Abduljabbar ya fitar da sautin muryarsa a karon farko yana cewa, “Idan har wadannan kalamai daga ni suke, kirkirarsu na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni na gaggauta tuba”.

“Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin wadancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban, sai mu yi rokon Allah ya haska wa al’umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan karya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su.”

Ni a fahimta ta wadannan kalamai na Abduljabbar rainin wayo ne a cikin su musamman inda yake cewa “Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin wadancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban, sai mu yi rokon Allah ya haska wa al’umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan karya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su.”

Lallai a nan akwai bukatar a duba sosai saboda nan yana nufin maganganun suna nan cikin littattafai duk da cewa malamai sun tambaye shi ya kasa nuna lattattafan da ya gani, akwai bukatar a sake titsiye shi.

Bayan mun fito mun haskawa gwamnatin irin tuban da yayi na karya ne sai ya sake sauya salo ya sake sakin sautin muryarsa a karo na biyu inda yace ya tuba, “Wadannan maganganu da suka fito daga bakina suka jawo ce-ce-ku-ce game da Ma’aiki SAW, na janye su na kuma janye su.”

Yana nufin ya janye kalaman sane don sun jawo ce-ce-ku-ce ba wai don yayi kuskure ba.

Abubuwan tambaya anan sune mai yasa bai ce yayi na dama ba, ya kuma yayi kuskure, me yasa bai tabbatar cewa maganganun sa babu su a litattafai ba?

Wadannan amsoshin muke nema a gurin sa.

Meye dalilin tuban Abduljabbar ?

Bisa nazari da nayi Abduljabbar ya tuba ne saboda ya fahimci hanyoyin samun kudinsa za su toshe tun bayan da yaran da yake tarawa su ka fara gane gaskiya suka fara watsayewa yaga cewa zai shiga wani hali na rashin kudi saboda ta hanyar sune yake samun kudi sakamakon shi dama bashi da wata sana’ar yi ko aikin yi sai dai ci da addini.

Daman yaran da yake tarawa suke tara masa kudi duk sati sannan kuma ta hanyarsu ne yan siyasa suke zuwa gurin sa don yana tara mutane, to ya gane an fara watsewa shi yasa yace bari ya tuba dan karya rasa su.

Don haka mutane a kula da shi sosai gwamnati karki yarda da wannan salo da ya sauya damfarace kawai cikin tuban sa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *