Worldcup 2022: Ingila Ta Lallasa Iran Da Ci 6 Da 2.

Page Visited: 70
0 0
Read Time:1 Minute, 58 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

An fara wasa tsakanin Ingila da Iran ne da ƙarfe biyu agogon Najeriya, a wasan farko na rukunin B na gasar cin kofin duniya na 2022 a filin wasa na Khalifa International Stadium da ke Qatar.

Mintuna 35 bayan take wasan, Ingila ta fara zurawa Iran kwallo ta ɗaya, ta hannun ɗan wasanta J.Bellingham, inda kuma ta ƙara sa kwallo ta biyu ta hannun B.Saka a mintuna 43.

Kwallo ta uku ta shiga ragar Iran ne mintuna biyu tsakani da kwallo ta biyu ta hannun  ta hannun R.Siterlling wato a mintuna 45, da fara wasan.

Daga bisani an tafi hutun rabin lokaci Iran na nema a hannun Ingila bayan ta ci ta uku kafin tafiya hutun.

Jim kaɗan bayan dawowa hutun rabin lokaci minti 62 da take wasa kwallo ta huɗu ta shiga ragar Iran wanda ɗan wasan B.Saka ya sake zurawa, wato yaci kwallo biyu kenan a wasan.

Iran ta fara farke kwallo ta ɗaya ta hannun ɗan wasanta M.Taremi a minti na 65.

Ingila ta ƙarawa Iran kwallo ta biyar ne a mintuna 71 ɗan wasan Ingila M.Rashford ya ci kwallon, a minti 90 kuma ɗan wasan Ingila M.Grealish ya saka kwallo ta 6.

Iran ta farke kwallo ta biyu ne lokaci kaɗan kafin tashi daga wasan wanda M.Taremi ya sake ci, wato dai shima ya ci kwallo biyu kenan a wasan.

Ecuador Ta Zargawa Qatar Mai Masaukin Baki Kwallo 2 A Raga.

Wannan dai shine wasa na biyu a gasar cin kofin duniya na shekarar  2022 kuma shine wasan farko a rukunin B.

A halin yanzu ƙasar Ingila ce ta farko a rukunin B da maki uku, inda Iran ɗin ke ta ƙarshe a tubur bayan ta yi rashin nasara.

Ingila za ta buga wasanta na biyu ne a rukunin B da ƙasar Amurka a ranar 25 ga watan Nuwamba, inda ita kuma Iran za ta sake buga wasa da ƙasar Wales a ranar ta 25 ga watan Nuwamba na 2022.

A halin yanzu dai ana buga wasan Senegal da Netherlands cikin rukunin A, kuma shine wasa na biyu a rukunin.

Ƙasar Qatar ce dai mai masaukin baƙi wadda tayi rashin nasara a hannun ƙasar Ecuador da ci biyu.

Wannan dai shine karo na 22 da ake buga kofin duniya na World Cup kuma karo na biyu a ƙasashen larabawa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Wasanni

Faransa Mai Ɗauke Da Kofin Duniya Za Ta Fara Kare Kofinta A Yau Talata

Daga Suleman Ibrahim Modibbo   Ƙasar Faransa mai dauke da kofin duniya za ta yi gumurzun kare kofinta da ƙarfe 8 ɗin daren yau a ƙasar Qatar a gasar cin kofin duniyar da ke gudana yanzu haka. Faransa ta ɗauki kafin ne a shekarar 2018 a ƙasar Rasha, bayan ta yi nasara a wasan ƙarshe. […]

Read More
Wasanni

A Halin Yanzu Tunisiya Ce Ta Ɗaya A Rukunin D Bayan Ta Yi Canjaras Da Denmark A Cigaba Da Gasar Cin Kofin Duniya.

  An kai ruwa rana tsakanin ƙasar Tunisiya da Denmark wanda hakan ya kai su ga tashi babu kwallo ko ɗaya a ragar ko wace ƙasa,, abinda ke nuni da cewa ƙasashen biyu suna tsaka mai wuya cikin rukunin D. Tunisiya za ta buga wasanta na gaba ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, inda […]

Read More
Wasanni

Saudiya Ta Fara Gasar Cin Kofin Duniya Da Kafar Dama Bayan Doke Argentina 2 Da 1.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.   Ƙasar Saudiyya ta zama ta ɗaya a teburin C bayan yin nasara a kan Argentina da ci biyu da ɗaya a wasan farko cikin rukunin C. Argentina ce ta fara cin kwallo ta farko a bayan mintuna 20 da fara wasan ta hanyar fanareti da samu wanda ɗan wasan gabanta […]

Read More