January 31, 2023

Yadda Ya Kamata Mai Tafiyar Kafa Ya Tsallaka Titi.

Page Visited: 69
0 0
Read Time:3 Minute, 14 Second

Rubutawa Suleman Ibrahim Modibbo

Na lura ana rasa lafiya, dukiyoyi, wani lokaci har ma da rai inda da karar kwana, sakamakon yadda mutane a kasar nan ke tsallaka titi cikin ganganci ko kuskure, kila kuma da sakacin hukumomi, don haka naga ya dace na yi wannan rubutu domin na ankarar da mutane su fahimci yadda ake tsallaka titi.

A dokar tsalla titi akwai hanyoyi guda biyu da mai tafiyar kafa ke bi don ya tsallaka titi, akwai Gada wato Bridge da kuma Fenti Mai Kama da Jikin Jakin Dawa Wato Mai Fari Da Baki da a turance ake kira da Zebra Cross Sing, duk wata hanya da kake bi ka tsallaka titi ba wannan za su iya zama matsala ga al`umma.

Da farko Gada ita ce duk wanda ya ke so zai tsallaka titi, akwai gudaren da ake yin wadannan gadoji domin su kawo sauki ga mai son tsallakawa musamman manyan hanyoyi, makarantu, kasuwanni, da guraren da kila jam`an tsaro ba za su kai ba, to sai ayi wannan Gada domin tsallakawar mai tafiyar kafa, hakan zai bawa mai abin hawa dama ya ba na kafa damar ketarewa ba ruwan kowa da kowa, kamar yadda zaku ga hoton gabar a kasa.

Wayewa shine a duk inda kaga an kafa wannan Gada kai mai tafiyar kafa kana son tsallawa, ka tsallaka ta kai shine wayewa, karshen rashin wayewa shine ka tsallaka ta hanyar masu ababan hawa.

Hanya ta biyu ita ce Fenti Mai Kama da Jikin Jakin Dawa Wato Mai Fari Da Baki da a turance ake kira da Zebra Cross Sing, duk inda kaga wanna to ya halarta ka tsallaka titi ta kan layin a ko ina a fadin duniya ba ma a iya Najeriya ba.

Yadda ake amfani da shi, shine idan kana son tsallaka titi sai kazo gaban sa ka tsaya, to, duk wani mai abin hawa da yazo wucewa zai tsaya cak har sai ka tsallaka sannan zai cigaba da tafiya, dole ne idan ka zo ka tsaya karka ce don tanan doka ta baka dama zaka tsallaka gaba gadi, a a ka jira tukum.

Su kuma masu ababan hawa dole ne su tsaya su jira, rashinn jiran karya doka ne ga kowa, kuma za a iya yiwa mutum gargadi ko kuma a hukunta shi, don haka ga masu ababan hawa idan sun tunkaro gurin wannan Zebra akwai bukatar dole sai sun rage gudu, don akwai alama da ake dasawa saboda sanar da direba kafin ya isa Zebra a nuna masa cewa a gaban sa zai tarar da wannan zebra dan haka ya rage gudu, idan kuma yazo zai lura hagu da dama idan babu mai bukatar tsallakawa sai ya wuce kawai, idan akwai sai ya dakata.

Akwai Zebran da kuma alamar d direba zai gani za ka ganshi a hotunan da suke kasaBin wannan doka shine wayewa, rashin bin wannan dokar zai iya zama rashin wayewa ko ganganci, wanda har mai tafiyar kafar zai iya fuskar hukunci ko gargadi.

Magana ta gaskiya yadda muke tsallaka titi kuskure ne, kuma yana jawo hatsari babba wanda mutum ya kan iya rasa lafiya, dukiya, da kuma rai, ba dai-dai bane mu dinga tsallaka titi ta ko ina, duk yadda muka ga dama.

Ita kuma gwamnati ya zama wajibi ta samar da wadancan hanoyoyin guda biyu , ta kuma tabbatar doka tana aiki a kan duk wanda karya ta ko na kafa ko wanda ke kan abin hawa, wajibi ne gwamnati ta tabbatar da ita gwamnati ce a kan kowa.

Akwai hanya wadda na kan Keke da na kafa suke tsallaka titi ta kai, a rubutu na naga zamu ji wacce hanya ce.

Irin wadannan abubuwa da muke raina sune idan muka sauke nauyin da ya ratawa a kan mu, muka bi ka ida za mu, samu shugabanni masu kishi da aiki da doka, saboda dama daga cikinmu shugabannin ke fita, Allah ya datar damu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *