August 8, 2022

`Yan Arewa Sun Yi Watsi Da Matsayar Gwamnonin Kudu Na Baiwa Yankin Kudu Shugabanci A 2023.

Page Visited: 226
0 0
Read Time:1 Minute, 0 Second

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi watsi da matsayar da gwamnonin yankin kudu suka cimma, na cewa wajibi ne shugaban kasa ya fito daga yankin kudu a zaben shekara ta 2023.

Kungiyar ta ce ba wani yanki da za’a ce tilas shi ne zai samar da shugabancin kasa a tsarin dimokaradiyya, domin kuwa mukami ne da ake zaben kowane mutum, kuma daga ko wane yanki ya fito.

A cewar kungiyar, kujerar shugaban kasa mukami ne da ake samu ta hanyar dimokaradiyya, ba wai tsarin karba-karba ba.

Kungiyar tana mai da martani ne akan matsayar da gwamnonin kudancin Najeriya suka cimma a wani taro da suka yi a birnin Ikko a ranar Litinin, inda suka ce tilas a baiwa yankin na kudu damar fitar da shugaban kasa, bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

VOA Hausa tace “Kungiyar ta amince abi mataki na bai daya cewa, a rika mulkin karba-karba tsakanin kudanci da arewacin Najeriya, ta kuma amince cewa, shugaban Najeriya na gaba, ya fito daga yankin kudanci.” In ji sanarwar da kungiyar ta fitar a karshen taron na Legas, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Odunayo Akeredolu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *