Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Rundunar ƴan Sandan jihar Kano, da ke Arewacin Najeriya, ta ce, ta gayyaci tare da tsare zaɓaɓɓen ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar Dala Aliyu Sani Madaki a ranar Laraba ɗaya ga watan Maris.
Mai magana da yawun rundunar Ƴan Sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.
A cewar yan sanda ana zargin Madaki da mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba “a yanzu haka yana sashin binciken manyan laifuka (SCID) na rundunar Ƴan Sandan jihar Kano, inda ake gudanar da bincike.”
Wasu hotun da suka dinga zaga kafafen sada zumunta sun nuna yadda aka ga Aliyu Sani Madaki rike da wata bindiga a hannun a ya yin taron yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Tinubu ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatinsa Akume
-
Kungiyar Ƴan Jarida ta ƙasa NUJ za ta bi sa sahun Kungiyar Kwadago NLC don Tsunduma yajin aiki kan cire tallafin Mai
-
Tsohuwar Ministar mata Pauline Tallen ta shiga hannun EFCC kan zargin Almundahana
-
Kotu Ta Bawa Ƴan Sanda Umarnin Kama Sheikh Idris Dutsen Tanshi Bisa Rainata.
-
Bayan Shan Rantsuwa Tinibu Ya Ce Daga Yanzu Gwamnatinsa Za Ta Soke Tallafin Man Fetur.