August 8, 2022

‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 40 Bisa Zarginsu Da Tashin Hankalin Al`umma Da Sunan Yajin Aikin Masu Adaidaita Sahu A Kano.

Page Visited: 998
0 0
Read Time:1 Minute, 21 Second

Daga: Suleman Ibrahim Moddibo

Rundunar ‘yan sandan jihar kano ta sanar da kama mutane 40 da ake zargin su da amfani da yajen aikin matuka babur din Adaidaita Sahu ke yi jihar wajen tayar da hankalin al`umma.

Kakakin rundunar ‘yan sandan na jihar kano DSP Abdullahi haruna kiyawa, ne ya tabbatar da kama wandanda ake zargin ga manema a shelkwatar ‘yan sanda ta dake Bambafai.

Kiyawa ya ce, “Yau 10 ga watan daya a wannan shekara ta 2022 da misalin karfe tara na safe muka samu rahoto cewa wasu bata gari sun fito wasu tiitina da ke wasu hanyoyin birnin kano, sun fake da yajin aikin da masu Adaidaita Sahu, suna tare hanya suna cin zarafin masu ababan hawa, ta`adi, tada hankalin al`umma, da kuma yin kwace.”

Yajin Aikin Adaidaita Sahu: Da Gaske Gwamnatin Kano Ba Ta Da Tausayi?

Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa 125, Ƴan Daba 1576 Da Ƴan Fashi 237 Cikin Shekarar 2021.

Ya kuma ce, bayan samun wannan rahoton “kwamishina ‘yan sandan jihar Kano Sama`Ila Shu`aibu Dikko, ya baza jami`an ‘yan sanda tare da basu umarnin duk wanda aka ga ya fito da makami ya tare hanya a kamo shi, wanda aka samu nasarar kama mutane 40 a gurare daban-daban wanda da zarar an kamala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu domin ayi musu hukunci.”

A safiyar ranar Litinin ne dai masu Adaidaita Sahu a jihar kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya suka tsunduma yajin aikin gargadi sakamakon zargin da suke hukumar Karota na takura musu, wanda ita hukamar ta Karota tasha musantawa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *