August 8, 2022

YANZU-YANZU: Bam ya tarwatsa yan Shi’a yayin Muzaharar Ashura, mutum 50 sun jikkata.

Page Visited: 214
0 0
Read Time:33 Second

Akalla mutum uku sun rasa rayukansu yayinda mutum 50 suka jikkata yayinda Bam ya tashi a tsakiyar mabiya akidar Shi’a yayin Muzahara a birnin Pakistan,a cewar hukumomi.

Aljazeera ta ruwaito wani babban jami’in gwamnatin birnin Bahawalnagar na cewa: “Muna masu tabbatar da labarin cewa mutum uku sun mutu yayinda 50 suka jikkata a tashin Bam.”

A shafukan sada zumunta, an ga bidiyoyin mumunar tashin Bam din yayinda jama’a ke kokarin taimakon wadanda suka jikkata.

Wani jami’in dan sanda, Kashif Hussain, ya tabbatar da wannan labari ga kamfanin dillancin labarai ta AFP. Inda yace: “Har yanzu bamu san yadda abin yake ba amma muna cigaba tattara bayanai daga wajen.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *