June 27, 2022

Zamu fatattaki cutar Korona kamar yadda muka yi wa cutar shan inna – Shugaba Buhari

Page Visited: 359
0 0
Read Time:39 Second

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada yunkurin kasashen nahiyar Afrika na kawo karshen annobar COVID-19 kamar yadda nahiyar tayi adabo da cutar shan inna wanda akafi sani da Polio.

Shugaba Buhari yayi wannan furuci be yayin taron kwamitin nahiyar Afrika na majalisar dinkin duniya wanda ya gudana ta kafar intranet, inda aka tabbatar da kawo karshen cutar ta Polio a hukumance.

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da sadarwa Femi Adesina ya hakaito shugaba Buhari yana ba da tabbacin ci gaba da mara baya wa kungiyoyin ba da agaji kamar su hukumar lafiya ta duniya wato WHO da asusun majalisar dinkin duniya da ke kula da ilimin yara wato UNICEF, da gidauniyar Rotary international da Gidauniyar Bill da Melinda hadi da gidauniyar Aliko Dangote da sauran su.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *