August 8, 2022

Zamuyi nazari kan Ingancin alluran Riga kafin Cutar Corona virus : JIBWIS Zaria

Page Visited: 497
0 0
Read Time:1 Minute, 14 Second

Daga: Mu’azu Abubakar Albarkawa, Kuduna

An gudanar da taron wayar da kai da Majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatuss Sunnah ta kasa reshen karamar hukumar Zaria.

Da yake bayyana makasudin taron, Shugaban Majalisar Malaman ta karamar hukumar Zaria, Sheikh Nura Zubairu Dambo, yace sun shirya taronne don sanin ko allurar rigakafi cutan mai sarkake numfani wato covid 19 yana da illa ko babu.

Kamar yadda gwamnati ta bayyana cewa za’a yiwa kowani Dan kasa riga kafin hana kamuwa da cutar.

Sheikh Nura Dambo, yace mun gayyato masana daga jami’o’i a kuma bangaren kula da magunguna da sa kula da lafiyar jiki, da kuma masana akan al-amuran yau da kullum, har ila yau mun gayyato malaman addinin musulunci don kallon abin a mahanga ta addini.

Malamin ya kara da cewa, zasu fitar da makoman su na amincewa ko rashin amincewar su da allurar rigakafin da zaran sun kammala hada bayanai.

Inda yace, zasu yi amfani da masallatai na hamsussalawati da na juma’a da kuma wuraren wa’azi da tarurruka don wayar da kan Jama’a.

Da yake nasa jawabin, babban limamin masallacin Juma’a na Madarkaci Sheikh Abubakar Jumare Gidado, yace zasu kalli abin ta mahanga na addinin musulunci.

Ya kuma yi kira ga likitoci musulmai da su taimaka masu wajen bincike don gano amfanin rigakafin ko rashin amfanin sa.

Taron ya sami halarta shehunnan malamai gada jami’ar Ahmad Bello Zaria da kwalejin horas da malamai dake Zaria, an dai yi taron ne a Jami’ar Ahmad Bello kongo zaria.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *