January 19, 2022

Zanyi Dukkan Mai Yiyuwa Wajen Samarda Tsaro A Jiha Ta- Lalong

Page Visited: 873
2 0
Read Time:42 Second

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya bayyana alhininsa a bisa harin da wasu suka kai a yankin karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato, a ‘yan kwanakin da suka gaba ta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da shi da takwarorin sa na jihohin Jigawa da Kebbi suka kai ziyarar ta’aziyya wa gwamnan jihar filato Simon Lalong.

Anasa jawabin, Shugaban tawagar wanda shine gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu yace manufar ziyarar tasu ita ce jajantawa al’ummar jihar bisa abunda ya faru.

Alh. Bagudu ya yabawa gwamnan jihar ta Filato Simon Lalong bisa matakin da ya dauka na tabbatar da tsaro a yankin.

Da yake maida jawabi, Gwamna Lalong wanda shine Shugaban kungiyar gwamnonin arewa, ya yaba musu bisa wannan ziyara, inda ya sha alwashin yin dukkan abunda ya dace don inganta harkar tsaro a jihar ta Filato.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *