January 31, 2023

Zargin Lalata: Sarkin Zazzau Ya Kori Ma’aikacin Fadarsa.

Page Visited: 135
0 0
Read Time:55 Second

Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa, Kaduna 

 

Majalisar Masarautan Zazzau karkashin Jagoranci Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ta bayar da umurnin Korar wani jami’intabMalam Sama’ila Abubakar Rimin Tsiwa, wanda ɗaya daga cikin Dogaran Fadar Zazzau daga aiki a Masarautanr.

A kori Dogarin ne bayan an zarge shi da yin lalata da wata matashi mai shirin yin aure bayan taje neman taimako gun sarkin Zazzau a fadar.

Wakilin Martaba FM a fadar ya ce “wata matashiya wanda take shirin Aure tazo Fadar Zazzau domin a sadata da Mai Martaba Sarkin Zazzau bisa neman taimako kan batun aurenta, ta gabatar da bayanan ta ga Malam Sama’ila wanda maimakon gabatar da ita zuwa inda ya kamata, sai ya yaudareta zuwa wani wuri dabam inda shi da abokansa suka yi lalata da ita.”

Zuwa yanzu dai Majalisan Masarautar Zazzau, ta umurci rundunan ƴan sanda da ta gaggauta kamalla bincike, kuma su gabatar da masu laifi cikin gaggawa a gaban Kotu domin yanke masu hukuncin dai-dai da laifinsu.

Haka kuma, Majalisan Masarautr Zazzaun ta dauki alkawarin bin sahun wannan batu domin tabbatar da an kwatarwa Matashiyar hakkinta.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *