September 22, 2021

Zaria : Mata da Matasa Samada 30 ne suka samu Tallafi sana’o’i daga Kungiyar Anguwar Malamai Progressive and Multi-Porpose Cooperative society. 

Page Visited: 293
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 32 Second

Daga: Mu’azu Abubakar Albarkawa Kaduna

 

An shawarci Iyaye da su sanya yaran su wurin koyon sana’o’i domin samun hanyoyin dogaro da kai.

 

Dakta Abdulhadi Gambo shine ya bada shawarar hakan, a lokacin da Kungiyar cigaban matasan Anguwan Malamai Tudun Wada Zaria a jihar Kaduna wato Anguwar Malamai Progressive and Multi-Porpose Cooperative sociaty ta shirya taron yayen daliban da ta koyar da su sana’o’i.

 

Yace, yin hakan zai taimakamawa har kan ilimi sana’a, dasu kan su Jama’a musamman mata da kananan yara.

 

Daktan ya yabawa ‘yan Kungiyar na irin kokarin da suke yi don cigaban Jama’an su, ya kara cewa, wannan ba karamin hobbasa bane, inda yayi kira ga masu hannu da shuni da su kawowa Kungiyar tallafi.

 

Da yake nasa jawabin, Dakta Sani Muhammad na Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ya godewa Jama’ar anguwar na irin goyan baya da suke bayarwa.

 

Inda yaja hankalin masu hannu da shuni dake anguwar, su taimakawa Kungiyar don cigaban ta.

 

Tun farko da yake nasa jawabin, Shugaban Kungiyar kwamared Badamasi Abdullahi ya bayyana irin nasarori da Kungiyar ke samu bayan kafa ta na tsawon shekaru biyu.

 

Yace, suna koyama mata yin jakunku na, zanin gado, bargo, Samar da aikin yi, tsaftace Anguwa, kula da tsaro da sauran ayyukan cigaban Anguwan.

 

Shugaban Kungiyar, ya kara da cewa wasu jama’an Anguwar basa Basu hadin kai Kamar yadda ya dace, inda ya roke iyayen yaran da su taimakawa Kungiyar.

 

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da horaswan, sun godewa Kungiyar na kokarin su na Basu horan da ya kama ta

 

Taron dai ya sami halartan Sarkin Gyallesu Alh. Aminu Sani da Prof. Salisu Muhammad Tahir da sauran manyan baki daga sassan Zaria da Sabon Gari.

 

An kuma karrama wasu fitattun mutane a Anguwan da suka bada gudumm uwa don cigaban Anguwan.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us