Wani ɗan banga da ke aiki a unguwar Dei-Dei a cikin Karamar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya Abuja Mujahid Ibrahim mai shekaru 32, an ruwaito cewa ya harbe kansa yayin da yake bin sawun wani da ake zargi a yankin.
An bayyana cewa harsashin da ya fito daga bindigar sa ya ji masa rauni a ƙafafu, inda aka fitar da harsasai akalla bakwai daga jikin sa.
An ce yana jiran sakamakon hoton da aka yi masa don gano ko har yanzu akwai wasu harsasai a jikin sa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare a ranar Laraba, lokacin da shi da abokin aikin sa suka tare wani mazaunin unguwar da suke gadin, wanda ke aiki cikin dare.
Da yake magana a jiya a babbar Asibitin Kubwa inda aka garzaya da shi, Ibrahim ya ce wanda ake zargin ya shiga unguwar ne da ƙarfe 12 na dare, maimakon ƙarfe 11 na dare da al’ummar yankin suka yarda da shi.
Ya ce “Abokin aiki na da ya same shi ya yi ƙoƙari don ya sa ya fahimci dokar wanda hakan bai samu ba, amma maimakon ya yi biyayya sai ya fara tayar da hankali. A ƙoƙarin tsoratar da shi, na harhaɗa bindigata ina nuna ta zuwa sama. Daga baya na mayar da bindigar a kafaɗata, amma na manta ban dawo da ita ba. A yayin da nake gudu zuwa gare shi yayin da yake faɗa da abokin aiki na, bindigar ta harba wasu harsasai da suka same ni a ƙafafu.”
Shi ma da yake magana, abokin aikin sa da ya raka shi asibiti Ben Isaac, ya ce bayan faruwar lamarin mutumin da ake magana akan sa ya tsere, amma babban yayansa ya ɗauki nauyin kula da maganin sa da kuma duk wasu kuɗaɗen jinya.
Ya ƙara da cewa an ba shi wa’adin sa’o’i 24 don ya bayyana kan shi, ko kuma a kama shi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya