Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Ana samun ƙaruwar mata masu neman lasisin mallakar bindiga a Lebanon - Martaba FM Ana samun ƙaruwar mata masu neman lasisin mallakar bindiga a Lebanon - Martaba FM

Rahotanni daga Beirut sun nuna cewa yawan mata ƴan ƙasar Lebanon da ke neman lasisin mallakar bindiga daga Ma’aikatar Tsaro na ƙaruwa sosai.

Hakan faruwa ne a wani mataki na sabon yunƙuri daga mata domin kare kansu, kasancewa masu dogaro da kai, da kuma ɗaukar harbi a matsayin wasanni.

Cynthia Yaacoub, wata kwararriyar malamar koyar da harbi mai shekaru 33, ta bayyana cewa yawancin mata na ganin harbi a matsayin hanya ta samun ƙarfin gwiwa da kariya daga barazana, musamman masu mazajen da ke yin aiki a ƙasashen waje.

Yaacoub ta bayyana cewa “harbi ba wai kawai domin koyon kashe mutum ba ne, amma yana taimakawa wajen fahimtar darajar rayuwa da kula da hankali kafin ɗaukar wani mataki.”

Wasu daga cikin waɗanda suka shiga horon sun bayyana harbi a matsayin sabon abin da suke so, musamman mata masu shekaru 50 zuwa sama da ke son gwada sabbin abubuwa bayan cika nauyin uwa da iyali.

Yaacoub ta kuma ƙirƙiri shirye-shirye na musamman domin ranakun kamar Ranar Uwa da Ranar Mata ta Duniya, ind a ta jaddada manufar “ƙarfafa mata ta hanyar horon harbi.”

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *