Labarai
Trending

Hukumomi A Ƙasar Maroko Sun Yi Wa Manoma Tabar Wiwi Kusan Dubu 5 Afuwa.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.

Yayin da ƙasar Maroko ke bikin samun ƴancin kai, ma’aikatar shari’a ta kasar ta sanar da yi manoma tabar Wiwi kusan dubu 5 afuwa.

An samu manoman da laifin noma tabar Wiwi ba tare da wani izini ba daga hukumomi abin da kai ga tuhumar su.

An yi wa Manoman afuwa su sama da duba huɗu da 800 ne a jajibirin bikin ranar da Moroko ta samun ƴancin kai, in da Mai Alfarma Sarki Muhammad, na 6 ya dauki wannan mataki saboda dalilai na jinkai.

Wasu daga cikin Manoman dubu 4 da 831, tuni aka yanke musu hukuncin dauri a gidan yari bayan an tabbatar da laifukansu, yayin da ake gudanar da bincike a kan wasu, bisa dalilan cewa sun mallakin manyan filaye da ake gudanar da noman tabar wuiwui a cikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button