Labarai
Trending

Luguden Wuta Da Isra'ila Ke Yi Kan Gaza Sun Tilasta Rufe Manyan Asibitoci Biyu.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da halin da asibitoci ke ciki a yankin Zirin Gaza, inda rohotanni suka ce a ranar Asabar manyan asibitocin yankin biyu sun dakatar da aiki, saboda luguden wuta babu kakkautawa da Isra’ila ke yi da kuma matsalar man fetur.

RFI ta ce babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniyar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya yi gargadi kan halin da ake ciki na mummunan hadari ga asibitoci a yankin Zirin Gaza, yana mai cewa karin marasa lafiya, ciki har da jarirai da bakwaini na mutuwa.

Manyan asibitocin Gaza biyu, Al-Shifa da Al-Quds, duk sun rufe, saboda sojojin sari-ka-noken Isra’ila na ci gaba da luguden wuta kan duk wani da suka gani kusa da asibitin Al-Shifa, inda dubban mutane suka makale a ciki.

Ma’aikatar lafiyar Faladinu ta bayyana cewa tun a ranar Asabar janareton asibin na karshe ya daina aiki saboda rashin man fetur, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar bakwaini uku da kuma wasu majinyata hudu, kuma wasu jarirai 36 na cikin hadarin mutuwa.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya uku sun bayyana firgici game da halin da ake ciki a asibitocin, inda suka ce a cikin kwanaki 36 an samu akalla hare-hare 137 kan cibiyoyin kiwon lafiya a yankin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 521 da jikkata wasu 686 – ciki har da jami’an kiwon lafiya 16 da suka mutu da kuma jikkatar wasu 38.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button