March 11, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Matatar Dangote haɗin gwiwa da kamfanin mai na MRS za su sayar da fetur a kan N935 duk lita.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tasirin yarjejeniyar musayar danyen mai da Naira wadda ta haifar da rage farashin mai a Najeriya.

Kamfanin ya sanar da hadin guiwa da MRS don sayar da fetur a gidajen sayar da mai na MRS a duk fadin Najeriya a kan N935 kan kowace lita.

Daily Nigerian ta rawaito, hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito a shafukan sada zumunta na kamfanin a ranar Asabar, inda suka ce wannan hadin gwiwar na nufin tabbatar da cewa ragin farashin ya kai ga Al’umma kai tsaye.

Bankin Duniya ya ce har yanzu Najeriya ba ta kama hanyar yaƙi da rashawa ba.

“Yawancin maganganun da ake yi na suka a kan ƙudurin ba ana yin su ne bisa wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, illa shaci faɗi kawai”-Tinubu.

Sojojin Nijar sun kashe Mahara 29 a Tillaberi.

idan za’a iya tunawa dai tun a ranar Alhamis din data gabata ne , matatar mai Dake sarrafa gangar mai 650,000 a kowace rana ta sanar da rage farashin zuwa N899.50 ga ‘yan kasuwa masu sha’awar saye, tare da bayar da bashi domin saukaka tsarin saye.

Wannan ci gaban dai ya haifar da fafutukar farashi a bangaren kasuwancin man fetur, inda kamfanin NNPC ya sanar da rage farashin zuwa N899 kan kowace lita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *