Labarai
Trending

Yajin aiki: Jami'ar Bayero Da Ke Kano Ta Dakatar Da Jarabawa.

Daga Firdausi Ibrahim Bakondi

Jami’ar Bayero ta jihar Kano ta sanar da dakatar da duk wata jarrabawar kammala karatun digiri na farko a zangon farko na shekarar 2022/2023.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun muƙaddashin magatakardar jami’ar, Amina Abdullahi Umar.

Dakatarwar a cewar sanarwar ta biyo bayan yajin aikin da kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC suka shiga a fadin kasar.

Hukumar kula da jami’ar ta umurci dukkan daliban da su kwantar da hankalinsu tare da jiran umarnin komawa makaranta.

Sanarwar ta kara da cewa, tuni an fara jarabawar an kai rabi, kuma da zarar an kammala yajin aikin za a ci gaba da gudanar da jarrabawar.

Idan za’a iya tunawa a ranar Litinin ne kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta umurci mambobinta da su shiga yajin aikin.

Yajin aikin na zuwa ne a matsayin martani ga harin da ‘yan sandan Najeriya da gwamnatin jihar Imo suka kai wa shugaban kungiyar NLC, wato Joe Ajaero.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button