Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama ‘yan daba 12 da suka kai hari kan masu sallar Tahajjud a Layin Bilya, titin Makwa Rigasa Kaduna.
An kama su ne a ranar Juma’a da misalin karfe biyu na dare, bayan samun kiran gaggawa daga wani mai kishin kasa, wanda ya bayar da rahoton cewa wani gungun ‘yan daba dauke da makamai sun hadu daga unguwannin Malali Gabas, Tudun Wada, Rafin Guza, da Unguwar Baduko, domin kai hari kan masu sallah a cikin goman karshe na watan Ramadan.
Bayan samun rahoton DPO tare da tawagar ‘yan sanda, da rakkiyar kwamandan CJTF, sun garzaya wurin domin damƙe wadanda ake zargi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Mansir Hassan, ya bayyana cewa kafin isar su, maharan sun riga sun daba wa wani mai suna Usman Mohammad mai shekaru 23 wuƙa, wanda duk da an garzaya da shi asibiti domin kulawar gaggawa, ya rasu bayan ‘yan sa’o’i, inda likita ya tabbatar da mutuwar sa.
A sakamakon haka, ‘yan sanda sun kama mutum 12 kuma sun amsa laifin su na kai harin, tare da kwace makamai da dama daga hannun su.
Bincike an fara gudanar da bincike na musamman domin gano cikakken bayani kan lamarin da tabbatar da adalci.
A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda ta karfafa tsaro a wurare masu muhimmanci, musamman a kusa da masallatai da ake gudanar da irin wadannan salloli.
Kakakin ‘yan sandan ya bukaci jama’a da su kasance masu lura da kuma gaggauta kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga ‘yan sanda, domin hana aikata laifukka.
Haka kuma, rundunar ta gargadi duk masu aikata laifukka da su daina, domin za su fuskanci hukunci mai tsauri idan aka kama su.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya