Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Kungiyar Alkalan Najeriya (MAN), reshen jihar Cross River, ta shiga yajin aikin sai baba ta gani bayan kasa cimma matsaya da gwamnati kan buƙatunsu.
Za a fara yajin aikin ne a ranar Litinin 9 ga Disamba 2024, in da aka umarci dukkan alƙalan jihar da su daina gudanar da duk wani aikin ofis, ciki har da zaman kotu, har sai wani jarin bayani ya zo.
Jaridar GUARDIAN ta ruwaito cewa ma’aikatan shari’a sun bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnati a ranar 5 ga Nuwamba, 2024, don gargadin fara yajin aiki a ranar 27 ga Nuwamba.
Sun fara yajin aiki na gargadi na tsawon kwanaki uku domin jaddada buƙatunsu guda takwas ga gwamnatin Bassey Otu.
A cewar sanarwar, rashin cika buƙatun kungiyar daga bangaren gwamnati ne ya sa aka fara wannan yajin aiki.
Bukatun sun hada da ƙarin albashi da wasu batutuwan jin daɗin aiki guda 7.