Wasu ƴan bindiga da ba a tantance ba sun sace ƴan ƙasar Indiya biyar a yammacin ƙasar Nijar yayin wani harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 12, kamar yadda jami’an tsaro na Nijar da hukumomin Indiya suka tabbatar.
Harin ya faru ne kusa da ƙauyen Sakoira, wanda ke yankin kan iyaka tsakanin ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso – wurin da ke fama da yawan hare-haren masu tsattsauran ra’ayi.
Rahotanni sun ce waɗanda aka sace na aiki ne da wata kamfani daga Indiya da ke a aikin gina madatsar ruwan Kandadji da ke yankin Tillaberi.
Gwamnatin jihar Jharkhand da ke Indiya ta ce dukkan mutanen da aka sace ƴan asalin jiharta ne, kuma ofishin jakadancin Indiya da ke Nijar ya riga ya tuntubi hukumomin Najeriya da Nijar domin neman taimako wajen kubutar da su.
Ko da yake ba a bayyana waɗanda suka kai harin ba, a baya-bayan nan gwamnatin Nijar ta zargi ƙungiyar EIGS, reshen ISIS, da kai hare-haren da suka hallaka mutane da dama a masallatai da ƙauyuka.
Masana harkokin tsaro sun ce satar mutane ta ƙaru a yankin bana, in da wata mace daga Austria da kuma wata Ba-Switzerland suka bace a watan Janairu da Afrilu. A cikin watan Janairu ma, direbobi hudu daga Maroko sun ɓace a iyakar Nijar da Burkina Faso.