Daga Sani Ibrahim Maitaya
Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Kaduna ta bayyana cewa a ranar 17 ga watan Afrilu 2025 da misalin karfe 3:20 na rana, an samu sahihan bayanai daga wata amintacciyar majiya game da wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne wanda ke buya a Gida Abe cikin jihar.
DPO na ofishin Tafa ya gaggauta tura tawagar sa ta sintiri zuwa wurin bayan samun bayanan sirri, inda suka kama wani mai suna Isa Ibrahim mai shekara 30 da haihuwa.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Mansir Hassan, ya ce yayin bincike wanda ake zargin ya amsa cewa mamba ne a cikin wata kungiyar masu garkuwa da mutane da ke aiki a jihar Kwara. Ya bayyana cewa abokan aikin sa sun shiga hannun hukuma a Kwara, hakan yasa ya tsere zuwa Kaduna domin kafa sabuwar ƙungiya.
Haka zalika a ranar 17 ga watan Afrilu 2025 da misalin karfe 1:30 na rana, DPO na ofishin Saminaka ya samu sahihin bayani kan kasancewar wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa ‘yan ta’adda a kauyen Lamido, cikin ƙaramar hukumar Lere. DPOn ya hanzarta tura jami’an sa zuwa wajen.
Jami’an sun kama mutum biyu da ake zargi, Sani Liman mai shekara 23 daga Unguwan Fa Ramin kura, da Murtala Magaji (wanda ake kira “Seto”) mai shekara 25 daga Dambata a kauyen Galadimawa, duk daga ƙaramar hukumar Kauru ta jihar. Sun amsa cewa suna cikin wadanda ke aikata garkuwa da mutane a yankin.
“Har ila yau a ranar 18 ga watan Afrilu 2025, da misalin karfe 6:00 na yamma, DPO na ofishin Ikara ya samu bayani daga wata amintacciyar majiya game da wasu mutane biyu da ake zargin masu safarar bindigogi ne, kuma suna da makamai a tare da su. Cikin gaggauwa DPOn ya tura tawagar sa zuwa wurin.”
“Mutanen da aka kama su ne Bajo Badun mai shekara 40 daga Vom Quarters Jos a jihar Filato, da Magaji Abdullahi mai shekara 40 daga kauyen Bargi ƙaramar hukumar Bebeji ta jihar Kano. An kama su da bindigogi kirar AK-47 guda biyu da aka sarrafa cikin gida,” in ji shi.
Bugu da kari sanarwar ta kara da cewa a ranar 18 ga watan Afrilu 2025, da misalin karfe 4:30 na safe, yayin da tawagar sintiri ke gudanar da ayyukan ta na yau da kullum a kan hanyar Kauru-Pambegua, suka lura da wani mutum da ke dauke da jaka yana tafiya da hali mai ban shakku. Jami’an suka dakatar da shi domin bincike.
“Bayan binciken jakar, jami’an suka gano bindigogi biyu da aka sarrafa cikin gida da kuma wani doguwar sarƙa, wanda aka nannade su sosai a cikin jakar. Nan da nan aka kama mutumin tare da kayan da aka kwace. An gano sunan sa da Ishiyaku Ali mai shekara 30 daga Bakin Dutse, ƙaramar hukumar Kauru.”
DSP Hassan ya bayyana cewa duk wanda aka kama suna tsare a hannun ‘yan sanda kuma suna ba da hadin kai a binciken da ke gudana, tare da bayar da muhimman bayanai. Rundunar ta ce tana ci gaba da kokarin kamo sauran da ake zargi da suka tsere.
A karshe Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kaduna CP Rabiu Muhammad, ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar zata ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron rayukka da dukiyoyin jama’a. Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa aikin tsaro.