Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Katsina ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu satar motoci ne, ta kuma ƙi karɓar cin hancin naira miliyan ɗaya, tare da kwato wata mota da ake zargin an sato ta ne.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a birnin Katsina.
A cewar sanarwar yayin da ‘yan sanda ke gudanar da sintiri a kusa da kauyen Birnin Kuka, cikin ƙaramar hukumar Mashi ta jihar Katsina, jami’an da ke ƙarƙashin sashen tsaron iyaka Zone 4 Katsina, sun dakatar da wata mota kirar Toyota Corolla LE, mai launin kore, wadda Mubarak Kabir da Adamu Hashim daga unguwar Kurna, ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano ke tukawa.
Binciken farko ya bayyana cewa motar da ake tuhuma an sace ta ne daga birnin Abuja, kuma waɗanda ake zargin sun miƙa wa jami’an sintirin cin hancin naira miliyan ɗaya, domin su kubuta daga hukunci, amma jami’an suka ƙi karɓa.
Hakanan an kuma kwato motar da ake zargin ta sata ce, da kuɗi naira miliyan ɗaya, wayoyin salula guda uku, power bank guda ɗaya, da ɗaurin makullai.
Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano yadda waɗanda ake zargin suka shafe lokaci suna aikata laifukka, tare da sanar da al’umma halin da ake ciki.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Katsina CP Bello Shehu, ya yabawa jajircewar jami’an wajen tsayawa tsayin daka kan doka da nuna gaskiya da rikon amana.
Ya ƙara da tabbatar da aniyar rundunar na ci gaba da kare rayukka da dukiyoyin al’umma a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya, tare da mutunta haƙƙin ɗan adam da ɗabi’a mai kyau.