Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Abin da ya haddasa gobara a runbun ajiye makamai na barikin Sojojin Najeriya a Maiduguri - Martaba FM Abin da ya haddasa gobara a runbun ajiye makamai na barikin Sojojin Najeriya a Maiduguri - Martaba FM

Rahotannin da suka fara yaɗuwa tun a daren jiya daga birnin Maiduguri na jihar Borno sun tabbatar da jin karar fashe-fashe da harbe-harbe daga barikin Sojoji na Giwa, lamarin da ya jefa mazauna birnin cikin firgici da fargaba.

Manema labarai sun rawaito cewa, sai da komai ya tsaya cak a birnin na Maiduguri, in da mutane suka firfito da gudu daga gidajensu sakamakon ƙarar fashewar abubuwa masu ƙarfi.

Sai dai Mataimakin Gwamnan jihar Borno, Dakta Umar Usman Kadafur, ya tabbatar da faruwar lamarin, in da ya roki jama’ar birnin da su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa a cikin gidajensu.

A nata bangaren sojojin Najeriya ƙarƙashin rundunar Operation HADIN KAI ta fitar da sanarwa ta hannun ƙukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Kyaftin Reuben Kovangiya, in da ta bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga tsananin zafin da ake fama da shi a Maiduguri, wanda ya haddasa fashewar wasu kayan aiki na soji da ke ajiye a cikin barikin.

Kyaftin Kovangiya ya ce an shawo kan gobarar cikin lokaci da hadin gwiwar jami’an kwana-kwana da na sauran hukumomin tsaro, kuma an tura sojoji zuwa wuraren da abin ya shafa domin tabbatar da tsaro da kuma hana wasu bata-gari amfani da wannan dama wajen tayar da hankali.

Ya kuma bukaci al’umma da su guji yaɗa jita-jita da kuma ɗaukar wannan al’amari a matsayin harin ta’addanci, domin babu wani hari da aka kai a cikin Maiduguri, kuma komai ya na tafiya daidai.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *