December 9, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

An Shekara Sama Da 5 Ba A Ɗauki Malami Ko Ɗaya Ba A Jihohin Najeriya 18 Ba-NUT.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Kungiyar Malmai ta Najeriya NUT ta ce zuwa yanzu akwai jihohin Najeriya 18 waɗanda suka kwashe sama da shekaru biyar ba a ɗauki malamin makaranta ko guda ɗaya ba.

RFI rawaito cewa, hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da aka gaza samun daidaito kan ƙarancin malamai a fadin kasar, kamar yadda alƙaluman ƙungiyar suka nuna.

A baya-bayan nan, Hukumar Ilimin bai-ɗaya ta ƙasar UBEC ta koka bisa ƙarancin malamai a makarantun gwamnatin ƙasar, yayin da wata ƙididdiga ta nuna cewa a halin yanzu sama da Yara miliyan 47 ne ke yin karatu a makarantun firamare da ƙananan sakandare na ƙasar dubu 171 da 27 masu zaman kansu da na gwamnati.

Gwamnatin Neja Ta Janye Dakatar Da Haƙar Ma’adinai A Jihar.

Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga A Dazukan Kaduna Da Zamfara.

Hukumar ta UBEC ta ce adadin makarantun gwamnati dubu 79 da 775 ne, yayin da makarantu masu zaman kansu suka kai dubu 91 da 252.

A cewar UBEC, a halin yanzu malamai dubu 354 da 651 ne ke koyarwa a makarantun Nursary, yayin da dubu 915 da 593 ke aiki a makarantun firamare, sannan dubu 416 da 291 ke aiki a ƙananan makarantun sakandare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *