Fadar Shugaban Ƙasa ta kare tsarin naɗe-naden mukamai da Shugaba Bola Tinubu ya yi, tana mai cewa rarraba mukaman da aka yi kwanan nan ya nuna adalci a tsakanin yankunan Najeriya, inda Arewa ta samu adadi mai yawa fiye da Kudu.
A cewar Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Watsa Labarai da Hulɗar Jama’a Sunday Dare, Shugaba Tinubu ya naɗa mutum 71 daga Arewa da kuma mutum 63 daga Kudu a manyan mukamai na gwamnatin tarayya.
Dare ya bayyana hakan a shafin sa na X a ranar Talata, a yayin da ake ci gaba da muhawara kan rashin daidaito na kabilanci a cikin nade-naden gwamnati.
Ya ce Shugaba Tinubu ya jajirce wajen tabbatar da adalci, ƙwarewa da haɗin kan ƙasa a cikin dukkanin yanke shawarar da ya ke yi, yana mai jaddada cewa ba wata ƙabila ko addini da ke rinjayar da shi.
“Mutane na kallon sabbin nade-naden da Shugaban Ƙasa ya yi ne ta madubin ƙabila kawai,” in ji Dare. “Amma yanzu yayi wuri a yanke hukunci cewa nade-naden ba daidai ba ne. Tinubu bai cika shekaru biyu a ofis ba, kuma akwai sauran nade-nade masu yawa da za su zo.”
Cikakken bayani kan naɗin mutanen Kudu na mutane 63 ya nuna cewa, Kudu maso Yamma ke kan gaba da mutum 26, sai Kudu maso Kudu da mutum 21, sannan Kudu maso Gabas mutum 16.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya