Babu Wata Barazana Game Da Ƙarancin Mai A Najeriya,-Manyan Dillalan Man Fetur.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Manyan dillalan man fetur a Najeriya, sun tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa akwai wadattacen man fetur a ƙasar, don haka ‘yan ƙasar su kwantar da hankalinsu.

BBC ta rawaito, Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar manyan dillalan, Clement Isong, ya fitar ranar Laraba ya ce akwai wadattacen mai a rumbunan ajiyar matatar mai ta Dangote da na babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL.

Isong ya ƙara da cewa babu wata barazana game da ƙarancin man fetur a ƙasar.

A makon nan ne dai kamfanin mai na NNPCL ya ƙara farashin man fetur a ƙasar.

Ƴan Kasuwar Man Fetur Sun Fara Siyen Man Daga Matatar Dangote.

APC Ta Gargaɗi Gwamnan Kano Kan Gudanar Da Zaɓe Ƙananan Hukumomi Gobe Asabar.

Kotun Ɗaukaka Ƙara A Kaduna Ta Sanya Ranar Fara Shari’a Kan Rikicin Sarauta A Masautar Zazzau.

To sai dai duk da haka an riƙa ganin dogayen layuka a wasu gidajen man ƙasar, wani abu da ya ƙara haifar da fargabar ƙaruwar farashin man a zukatan ‘yan ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Proudly powered by WordPress | Theme : News Elementor by BlazeThemes