Daga Suleman Ibrahim Modibbo.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Celta Vigo ce ke jagoranta teburin Laliga a mataki na ɗaya da maki 3, bayan da ta doke Alves da ci 2 da 1 a wasan da suka buga na farko a ranar Juma’ar da ta gabata.
Barcelona ce ke biye mata a mataki na biyu da maki 3, bayan ta yi nasara a wasan da ta buga ranar Asabar da Valencia, in da ta ci 2 da 1.
Ita ma ƙungiyar Rayo Vallecano, ta na da maki 3, kuma ita ce ke riƙe da mataki na uku a gasar ta bana, ta kai wannan matsayi ne bayan ta yi nasara a kan Real Sociedad da ci 2 da 1.
Las Palmas ce ke a mataki na huɗu yayin da ƙungiyar Sevilla ke mataki na biyar, Girona a mataki na 6, ita kuma Getafe ke mataki na 8, dukkansu da maki ɗai-ɗai.
A daren jiya ne Lahadi ne ƙungiyar Real Madrid ta buga canjaras a wasan da ta fafata da Mallorca, in da suka tashi
1-1 a wasan farko na La Ligar bana.
Real Madrid na mataki na 12 ya yin da Mallorca ke mataki na 8 da maki ɗai-ɗai.