Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), reshen jahar Lagos ta gurfanar da karin yan kasar Chaina su 16 a gaban Mai Shari’a Daniel Osiagor na Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi Lagos, bisa zargin damfara.

Waɗanda aka gurfanar din na daga cikin mutane 792 da ake zargi da damfarar kuɗaɗe na yanar gizo, waɗanda jami’an EFCC suka kama a Lagos a ranar 10 ga watan Disamba 2024, a wani samame da aka kira “Eagle Flush Operation”.

Bayanin gurfanar da su ya fito ne cikin wata sanarwa da hukumar yaki da cin hancin ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata.

Waɗanda aka kama sun hada da Hu Hui wanda aka fi sani da A Bin, da Liao Ri Xing (a.k.a. Li Jun), Li Qiang wanda aka fi sani da Yang Huan Huan, da A Wen, da Da Tou, da Cheng Jian, da Cong Bing, da Fei Fan, da Huxi Heng, da Zheng Wei wanda aka fi sani da A Hong, da Huang Zhi, da Zhang Lei, da Sun Zhi Peng, da Huang Jin Hui, da Wù Hao, da kuma Lu Qiang.

Sanarwar ta kara da cewa an gurfanar da su kan laifuka daban-daban da suka haɗa da laifukkan zamba ta intanet, da ta’addanci ta intanet, da mallakar takardun ƙarya, da damfarar kuɗin gabanin wani aiki (advance fee fraud), da satar bayanan mutum.

Dukkan waɗanda ake tuhumar sun musanta laifukkan da ake tuhumar su da su. Bayan haka lauyan EFCC Nnaemeka Omewa, ya bukaci kotu ta sanya ranar fara shari’a tare da ba da umarnin tsare su a gidan gyaran hali.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *