Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar SDP Malam Nasir El-Rufai, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya mayar da zababbun jami’ai a jihar Ribas.
El-Rufai wanda ya yi wannan kira a shafin sa na Facebook a daren Laraba, ya ce yana da hadari ga tsarin dimokuradiyyar tarayya a kasar nan, idan shugaba da aka zaba ya dauki iko da cire zababbun jami’ai a matakin jiha.
Tsohon gwamnan ya ce nauyin da ke kan shugaban kasa yana da girma kuma ya kasance cikin iyakokin kundin tsarin mulki da dokoki, wadanda ba su hada da sallamar mutanen da al’umma suka zaba ba.
El-Rufai ya ce “Akwai abubuwa da suka bayyana a matsayin kuskure, kuma duk wata hujja da za a kawo don kare su ba za ta tsaya daidai ba. Matakin da Shugaban Kasa ya dauka na dakatar da zababbun jami’an gwamnatin jihar Ribas yana daga cikin irin wadannan kura-kurai.
Ya ce “Tabbas matsalolin tsaro da aka ambata a jawabin Shugaban Kasa sun cancanci a dauki matakin gaggawa domin dakile barazanar, da kuma kare muhimman kayayyakin kasa. Wannan nauyi ne da ya kamata mu mara wa hukumomin tsaro baya domin su sauke shi cikin nasara’.
Ya kara da cewa “Akwai damar ayyana dokar ta-baci don bai wa hukumomin tsaro iko na musamman da kuma yin amfani da albarkatun da suka dace don su magance matsalar. Amma fadada ikon dokar ta-baci har ya kai ga rushewar tsarin dimokuradiyya tamkar take dokoki ne da ka’idojin mulkin dimokuradiyya. Kotun Koli ta riga ta yanke hukunci a shari’ar Dariye da Antoni Janar na Tarayya cewa dakatar da zababbun jami’an baya kan ka’ida.
“A ra’ayina ya kamata Shugaban Kasa ya sake duba wannan matsaya ya koma kan bin doka da oda. A matsayinsa na dan adawa a baya, Sanata Bola Tinubu ya fito fili ya soki matakin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan na ayyana dokar ta-baci a yankin Arewa maso Gabas, duk da cewa wannan matakin bai kai ga dakatar da zababbun jami’ai da hukumomi ba”. Inji tsohon gwamnan.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya