Daga Fatima Suleiman Shu’aibu.
Wasu rahotanni daga kafafen yaɗa labarai qa Najeriya na cewa, tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya mallaki rukunin gidaje 753 da EFCC ta ƙwace a Abuja.
Tun da farko a ranar Litinin hukumar EFCC ta ce ta samu nasarar karɓe gidajen a hannun wani tsohon babban jami’in gwamnati wanda bata fadi sunanshi ba.
Amma wasu takardun shigar da ƙara sun nuna cewa gidan na dakataccen gwamnan babban bankin Nijeriya ne Godwin Emefiele wanda ke fuskantar shari’a.
A cikin takardun kotun da wakilin Jaridar PUNCH ya samu a ranar Talata, EFCC ta bayyana yadda ta gano wannan gida mai girman murabba’in ƙasa 150,500, wanda ke a Plot 109, Cadastral Zone C09, Lokogoma District, Abuja.
To amma an yi ƙoƙarin samun martanin daga lauyoyin Eefiele ya ci tura, domin Matthew Burkaa (SAN) bai amsa kiran waya ko saƙon tes ba a lokacin haɗa wannan rahoto.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya kare dalilin hukumar na boye sunan mai gidan, ya ce dokar da aka yi amfani da ita ta ba da damar kwace dukiya ba tare da ambaton sunan wanda ke da ita ba, musamman idan babu wanda ya nuna mallakar abu.
Ya kara da cewa binciken kan al’amarin bai kammala ba, kuma bayyana sunan waɗanda ake zargi ba zai dace ba a wannan matakin
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.
-
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.