Labarai
Trending

Gayyatar Joe Ajaero Yunƙurin Tursasa Wa NLC Ne Kan Ta Yi Abin Da Gwamnati Ke So-Amnesty.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Yayin da rundunar Ƴansandan Najeriya ta gayyaci shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasar Joe Ajaero, ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya ta nuna damuwa kan sabbin zarge-zargen taimaka wa ta’addanci da hukumomi ke yi kan ƙungiyar ƙwadago.

Cikin wata takardar sanarwa da ta fitar, Amnesty ta soki yunkurin hukumomin gwamnati da cewa matakin da rundunar ƴansandan Najeriya ta ɗauka na gayyatar Ajaero wani yunƙuri ne kawai na tursasa wa NLC ta yi abin da gwamnati ke so.

BBC ta ce, Amnesty International ta buƙaci hukumomin da su mutunta ƴancin ƙungiyoyin ƙwadago domin bayyana ra’ayoyinsu, ta kuma yi gargaɗin a guji amfani da ikon gwamnati wajen rufe bakin kungiyar ta NLC.

Ita ma nata ɓangaren ƙungiyar kwadagonta yi gargaɗi tare da yin barazanar fara yajin aikin sai baba-ta-gani, idan har aka kama shugabanta, Joe Ajaero.

Ƙungiyar ta yanke wannan shawarar ne a wani taron gaggawa da jagororinta suka gudanar a yau, Talata.

NLC ta bayyana zarge-zargen aka yi wa Ajaero a matsayin marasa tushe, kuma ta yi zargin cewa lamarin na da alaƙa da siyasa.

Ƙungiyar ƙwadagon ta zargi mahukuntan Najeriya da yunƙurin tursasawa da kuma musguna wa shugabanninta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button