April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnatin Cross River ta gargadi shugabannin ƙananan hukumomin jihar kan biyan albashin malaman makaranta.

Kwamishinan Ilimi na jihar Cross River Stephen Odey, Associate Farfesa, ya gargadi shugabannin ƙananan hukumomi 18 na jihar da su kula da illar rashin biyan albashin malaman makaranta.

Odey ya bukaci shugabannin ƙananan hukumomi da su baiwa biyan albashin malamai muhimmanci, domin ƙarfafa ƙwazon su a aiki.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya yi tare da shugaban Hukumar bada Ilimin bai daya ta jihar, da shugabannin ƙananan hukumomi da kuma ma’aikatar sa a Calabar ranar Talata.

Ya jaddada cewa biyan albashin malammai akai-akai yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙara ƙwazon su.

“Ko da albashin ba wani yawa bane, idan ana biyan sa akai-akai, yana da matuƙar muhimmanci,” in ji Odey.

Ya ƙara da cewa hukuncin Kotun Ƙoli ya sanya wajibci ga shugabannin ƙananan hukumomi su baiwa biyan albashin malamai muhimmanci, saboda kuɗaɗen malamai suna shiga asusun ƙananan hukumomi kai tsaye.

Odey ya bayyana cewa Hukumar SUBEB ta jihar Cross River ta samu nasarori da dama lokacin da yake shugabancin hukumar, inda ya jaddada cewa hakan ya samu ne sakamakon biyan albashin malamai akan lokaci.

“Na tuntubi ƙwararren masanin ICT wanda zai ƙirƙiri manhaja domin in riƙa bin diddigin yadda ake biyan albashin malamai. Da dannawa kawai daga ofishi na, zan iya ganin duk albashin da aka biya malamai a kan dashboard ɗina,” in ji shi.

A nasa jawabin Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi na jihar, wanda kuma shi ne shugaban ƙaramar hukumar Yala Mista Yibala Inyang, ya nemi a baiwa shugabannin ƙananan hukumomi dama su ɗauki karin malammai a yankunan su domin farfaɗo da sashin ilimi a kananan hukumomin su daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *