Gwamnatin jihar Kebbi ta karyata zargin cewa jihar tana da mutane dubu goma sha biyar da ɗari tara da saba’in da tara, da aka yi wa rijista a matsayin masu luwadi da kuma dubu goma sha takwas da ɗari biyar da sittin da bakwai da aka yi wa rijista a matsayin ‘yan maɗigo.
Gwamna Nasir Idris ya karyata wannan zargi ne yayin da yake mayar da martani, ga wani wa’azi da babban Sakatare mai kula da majalisar Zartarwa a Birnin Kebbi, Dokta Nasir Kigo ya gabatar, a wurin wani taron addinin Musulunci.
A cikin bidiyon wa’azin da ya wallafa a shafin sa na Facebook, babban sakataren ya yi zargin cewa a lokacin ƙidayar farko alkalumma sun nuna cewa, jahar Sakkwato ta kasance ta biyu a Najeriya baki ɗaya dake da mutane 9,978 da aka yi wa rijista a matsayin masu luwadi.
“Sakkwato tana da ‘yan madigo 10,456 da aka yi wa rijista, kuma sun kasance na ukku a ƙasar.
Ya ce “A jahar Kebbi, mutane 1,088 aka yi wa rijista gaba ɗaya a matsayin masu luwadi a ƙidayar farko, yayin da 7,986 suka kasance ‘yan madigo da aka yi wa rijista.
“Amma a lokacin ƙidayar da ta biyo baya, Kebbi tana da 15,979 da aka yi wa rijista a matsayin masu luwadi, tare da 18,567 da aka yi wa rijista a matsayin ‘yan madigo,” in ji shi.
Gwamnan wanda ya nuna rashin jin daɗin sa kan waɗannan alkalumma da babban sakataren ya bayar, ya ce adadin ba su da tushe kuma ba su da wata hujja da ke tabbatar da su.
“Bayan bincike mai zurfi, gwamnati ta gano cewa wannan bayani ba gaskiya ba ne. Don haka, muna kira ga al’umma su yi watsi da wannan bayani domin ba shi da wata hujja,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnati za ta ɗauki mataki kan babban sakataren da ya fitar da wannan bayani maras tushe.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya