Wani hadari mai karfi da iska sun lalata gidaje da dama a garin Dakin Gari, karamar hukumar Suru ta jihar Kebbi.
A cewar wani mazaunin garin Dakin Gari Umar Wali, hadarin ya zo tare da ruwan sama mai yawa, ya rushe gidaje da dama da har yanzu ba a tantance adadin su ba.
Yayin da hukumomi ke ci gaba da duba yawan gidajen da abun ya shafa da kuma halin da mazauna suka tsinci kan su, wakilin mu ya tabbatar da cewa hadarin ya lalata gidajen mata biyu, inda su ma suka sami raunukka masu tsanani.
Baya ga matan da abin ya shafa, Arewa PUNCH ta kuma samu labari daga Umar cewa, wasu yara da dama na karbar magani a asibiti a Dakin Gari, sakamakon raunukkan da suka samu lokacin da katanga ta fadi a gidajen su.
Wanda ya shaida lamarin ya shaida wa wakilin mu cewa: “Eh, mun fuskanci iska mai karfi da ruwan sama wanda ya zubar da rufin gidaje da dama, ya rushe wasu gine-gine, kuma ya jikkata mata da yara da dama.”
Sai dai ya ce bai tabbatar ko Gwamnatin jihar Kebbi da hukumominta sun samu labarin lamarin ba, ko kuma sun dauki matakin rage radadin barnar ba.
A halin yanzu wakilin mu ya tabbatar da cewa Shugaban Karamar Hukumar Suru Alhaji Muhammad Lawal Suru, bai kai ziyara Dakin Gari ba har lokacin da ake hada wannan rahoto.
Idan ba’a manta ba jahar Kebbi na daya daga cikin jihohi shidda da aka yi hasashen za su fuskanci ruwan sama mai yawa a bana.