April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Jami’an tsaro a Zamfara sun ƙaddamar da farautar Ƴanbindiga a wani yankin jihar bayan sun yi ajalin mutum biyu tare da sace wasu 26.

Jami’an tsaro sun kaddamar da farautar Ƴanbindiga a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, bayan harin da suka kai kauyen Banga, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da sace wasu 26.

Wani mazaunin yankin, Ahmad Ɗan Baba Adamu, ya shaida wa Radio Nigeria cewa maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare, in da suka fara harbe-harbe ta ko ina har zuwa ƙarfe ɗaya da minti Arba’in na dare ranar Laraba.

“Sun kashe wani mutum mai suna Ibrahim Kafinta da wata yarinya mai shekaru 18 mai suna Amina Mande. Sannan sun sace mata 14 da maza 12, wanda ya kai jimillar mutane 26,” in ji shi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa rundunar sojoji da haɗin guiwar ‘yan sa kai sun rufe hanyoyin ficewar ‘yan bindigar a yankin Yamutsawa, tare taimakon dakarun sojin saman Najeriya. Duk da haka, har yanzu ba a cimma nasarar cafke su ba.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, DSP Yazid Abubakar, ya ci tura, domin bai amsa kiran wayarsa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *