Kamfanin sadarwa mafi girma a Najeriya, MTN, ya bayyana cewa ya zuba jarin naira biliyan 202.4 a cikin watanni uku na farkon shekarar 2025 domin ƙarfafa cibiyoyin sadarwarsa.
Wannan ya nuna ƙaruwa da kashi 159% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, sakamakon amincewar hukuma da ƙarin kuɗin sabis da ya kai kashi 50%.
Kamfanin ya bayyana hakan a cikin rahoton kuɗadensa na rabi na farko na shekara, in da ya ce jarin zai taimaka wajen inganta sabis da magance karancin damar sabis sakamakon yawaitar amfani da intanet daga masu amfani da ke kai miliyan 84.
Har ila yau, kamfanin MTN sun rattaba hannu kan yarjejeniyar amfani da tsare-tsaren gini tare da Airtel Africa domin faɗaɗa isar sadarwa da rage farashi.
A cikin wata sanarwa, Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bayyana cewa kamfanonin sadarwa sun riga sun ba da oda da ya kai dala biliyan 1 daga masana’antun China domin sabunta ingancin ayyuka, kodayake kayan ba su iso ba tukuna.
Kamfanin ya samu riba ta naira biliyan 133.7 a cikin wannan lokaci, idan aka kwatanta da asarar naira biliyan 392.7 da ya yi a bara. Hakan ya faru ne saboda ƙaruwar ribar aiki da kuma raguwar asarar da ta shafi musayar kudin waje.